Videos

Motocin da za’a Bayar a Gasar jagaban tsofaffine korafin mutane zuwa ga Mawaki Rarara

Motocin da za’a Bayar a Gasar jagaban tsofaffine korafin mutane zuwa ga Mawaki Rarara

Babu shakka mawakin yaji koke koken jama’a akan gasar dayasa amma kuma ya kasa cika alkawari wanda mutane suka fusata suka dinga yi amsa mummunan martani da kuma bakaken maganganu akan wannan abu domin yayi harka ta kananun mutane bayanda ake masa kallon babban mutum amma yaso ya mayar dakansa karamin mutum

A wannan lokacin nagansa yana yunkurin cika wannan alkawarin domin daman kowa yasan cewa alkawari kayane duk wanda yayi be cikaba akwai hisabi tsakninsa da Ubangijinsa ranar gobe kiyama don haka jama’a mu daure muna cika alkawari

Mawakin Yasa kyautar motoci gaduk wanda suka hau kan sabuwar wakar da yayiwa Tunibu mai suna Jagaban wanda kuma an samu mutane fiye da dari sun hau kan wannan wakar amma kuma daga baya yayi biris dasu kai kace besan zance ba wanda hakan yasa hatta masoyansa suka dinga yi masa korafi akan wannan abin

Yanzu yaji wannan abubuwan domin a yanzu haka motoci sun iso garin Kano kuma za’a fara bayarwa ga duk wanda yasan yaci wannan gasar kuma an tantamceshi saiya shirya domin motoci sun samu zuwa

Sai dai abin kalla anan shine yadda ake ta korafi akan wa’yannan motoci don anzaci za’aga sababbin motoci sai kuma kawai akaga wasu tsofaffi kome yasa haka zamu jira muji daga bakin mawaki rarara

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button