Mu Da Gwamnati Muke Amfana Da Matsalar Tsaro, Cewar Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Abu Sani

Mu Da Gwamnati Muke Amfana Da Matsalar Tsaro, Cewar Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Abu Sani
Wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai satar mutane a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ya ce matsalar rashin tsaro na ƙara ta’azzara ne a arewacin ƙasar saboda an mayar da lamarin na neman kuɗi
Abu Sani wanda shi ne ya jagoranci sace ƴan matan sakandaren gwamnati ta garin Jengeɓe a bara, ya faɗi hakan ne a wani shiri na musamman na binciken ƙwaƙwaf da ta gudanar kan ayyukan ƴan bindigar
A yau Litinin ne BBC ta saki shirin na Africaa Eye a shafukanta na sada zumunta cikin Hausa da Turanci An mayar da abin neman kuɗi a wannan ɓangare, kowa kuɗi yake nema,shi ya sa harkoki suke lalacewa, tun daga manyan har zuwa ga ƙananan in ji ɗan bindigar
Su kuma jami’ai su ma gwamnati idan ana rikici ana tura mata da kuɗi, ka ga ta wannan ɓangaren suna samu ke nan Mu ma ta nan duk da dai za a zubar da jini a yi rashe-rashe amma kuma a yi ta yi haka nan
A cikin hirar ya kuma bayyana cewa sai da gwamnatin Jihar Zamfara ta ba su fansar naira miliyan 60 kafin su saki ƴan matan sakandaren Jageɓe da suka yi garkuwa da su
Sai dai gwamnatin ta daɗe da musanta cewa ta bayar da kuɗi kafin a sako ƴan matan