ylliX - Online Advertising Network Mubarak Uniquepikin ya samu gurbi a gidan Yari, bisa zargin bata sunan Ganduje a wasan barkwanci. - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Mubarak Uniquepikin ya samu gurbi a gidan Yari, bisa zargin bata sunan Ganduje a wasan barkwanci.

Mubarak Uniquepikin ya samu gurbi a gidan Yari, bisa zargin bata sunan Ganduje a wasan barkwanci.

Dan wasan barkwanci, Mubarak Muhammad, wanda aka fi sani da Uniquepikin, tare da mai ja masa baki Nazifi Isa Muhammad, sun samu gurbin zama a gidan gyaran hali, bayan sun amsa laifinsu a gaban kotun majistare mai lamba 58 dake Normansland, karkashin jagorancin mai shari’a Jostis Aminu Gabari.

Tunda fari dai, hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano ce ta shigar da kara bisa zargin matasan da haɗa kai wajen bata suna da cin zarafin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, tare da yunkurin tayar da tarzoma a wani faifan bidiyo da suka fitar.

Rahoton Freedom Radio ya bayyana cewa, lauyan wadanda ake kara tare da iyayensu, sun roki alfarmar kotu ta yi musu afuwa, amma Alkali ya dage zaman shari’ar zuwa ranar Litinin 7/11/2022 domin cigaba da shari’a

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button