Warning: preg_match_all(): Compilation failed: missing closing parenthesis at offset 88 in /home/hausydwo/Amincihausatv.com/wp-content/plugins/seo-by-rank-math/includes/replace-variables/class-post-variables.php on line 545

Warning: preg_match_all(): Compilation failed: missing closing parenthesis at offset 88 in /home/hausydwo/Amincihausatv.com/wp-content/plugins/seo-by-rank-math/includes/replace-variables/class-post-variables.php on line 545
MUHIMMAN ABUBUWAN DA SUKA FARU A ZAMAN KOTU NA YAU 23/6/2022(Abin ya zo, inji mai tsoron wanka) - AMINCI HAUSA TV
Warning: preg_match_all(): Compilation failed: missing closing parenthesis at offset 88 in /home/hausydwo/Amincihausatv.com/wp-content/plugins/seo-by-rank-math/includes/replace-variables/class-post-variables.php on line 545

Warning: preg_match_all(): Compilation failed: missing closing parenthesis at offset 88 in /home/hausydwo/Amincihausatv.com/wp-content/plugins/seo-by-rank-math/includes/replace-variables/class-post-variables.php on line 545
LABARAI/NEWS

MUHIMMAN ABUBUWAN DA SUKA FARU A ZAMAN KOTU NA YAU 23/6/2022
(Abin ya zo, inji mai tsoron wanka)

MUHIMMAN ABUBUWAN DA SUKA FARU A ZAMAN KOTU NA YAU 23/6/2022
(Abin ya zo, inji mai tsoron wanka)

A yau aka zauna sauraron shari’ar Abduljabbar Kabara, wanda yau shi ne zama na 21 a cikin jerin ranakun da aka zauna.

A yau an buɗe sabon shafi a wannan shari’a. Domin yau ne lauyoyin gwamnati suka fara yiwa Abduljabbar tambayoyi, abinda ake kira Cross Examination.

A zaman na yau, abubuwa da dama sun faru, ga kaɗan daga cikinsu:-

  1. Batun kunna audion masu gabatar da ƙara: A zaman da ya gabata an kunna audio ɗin da Abduljabbar ya gabatarwa kotu. Kuma an nemi lauyoyin gwamnati su gabatar da Certificate akan nasu audios ɗin idan suna buƙata a kunna. A yau alƙali ya tambaye su, shin sun shirya kunnawa?

A nan lauyoyin gwamnati suka tabbatarwa kotu cewa sun shirya tsaf akan kunna audio, amma sai bayan sun kammala yiwa Abduljabbar tambayoyi. Alƙali kuma ya amince da hakan.

  1. Musu akan tuhuma: A ranar da Abduljabbar ya fara yin Defence, ya shaidawa kotu cewa a cikin tuhumar mas’alar HAJA, akwai abinda ya faɗa, kuma akwai abinda bai faɗa ba. Da aka tambaye shi me ya faɗa kuma menene bai faɗa ba? Sai yace “na fadi cewa wata mata ta zo tana kwarkwasa, kuma tace tana sha’awar Annabi (wal iyazu billahi) , kuma Annabi yace taje ta nemi duk inda take so zai je ya biya mata bukatar ta”. “Amma ban ce ya bita kwararo ya biya mata buƙata irin ta ɗa namiji da mace ba”. Inji Abduljabbar.

Cikin ikon Allah, wannan maganar da Abduljabbar ya musanta, tana cikin jerin datsatssun audios ɗin da ya gabatarwa kotu a zaman da ya gabata.

A yau, lauyan gwamnati, Sheikh Barrister Abdurrahman, ya sake dawo da maganar, inda ya tambayi Abduljabbar, “ka yarda ka fada ko har yanzu kana musu?” Abduljabbar ya ƙara musantawa, har sai da aka ɗauko record din kotu na ranar da ya fara musanta maganar, aka duba aka tabbatar da musun da yayi, sannan aka dawo kan audio.

Lauyan gwamnati, ya nemi kotu ta kawo Memory ɗin da Abduljabbar ya gabatar da kansa domin a kunna a tabbatar masa da abinda ya kore.

Kotu ta kawo memory, kuma lauyoyin gwamnati sun nemi a basu dama su gabatar da Awaisu Al’arabee Fagge domin ya kunna musu abinda yake cikin memory ɗin. Kuma alƙali ya amince.

An fara kunna muryar Abduljabbar, kuma kotu ta fara jinsa yana faɗar abinda ya musanta cewa bai faɗa ba, sai ya tayar da hayaniya, wai me kunnawar (Awaisu) ya datse/wuce farkon maganar. Kamar wasa abu ya zama ƴar ƙaramar hayaniya. Aka ce masa wannan fa memory ɗin da ka gabatar ne, ba su suka kawo ba, amma ina… Abduljabbar ya tayar da yamutsi akan lallai an datse masa. Hayaniya ta yawaita, wasu ma suka fara maganar a bashi ya kunna da kansa, har dai daga ƙarshe alƙali ya bada hutu na ɗan lokaci.

Bayan an dawo daga hutu, alƙali ya ɗan yi nasiha ga dukkan bangarori biyu na lauyoyi, kuma ya kara bada umarni ga Awaisu akan ya ƙara kunnawa kowa ya ji.

An kunna Audio din tuhumar da Abduljabbar ya musanta, kuma an yi amfani ne da Memory ɗin da ya gatabar, kowa yaji. Sannan kuma daga baya ya amince cewa mai kunna Audio bai datse masa komai ba. Sai aka tambaye shi, yanzu ka amince ka fadi waɗancan kalaman?
“Ni fa korewa nake yi ba tabbatarwa ba”, inji Abduljabbar.

Haka dai aka kama shi ƙiri-ƙiri yana gujewa abinda shi ya faɗa da bakinsa, kuma ya gabatarwa da kotu.

A wannan gaɓar, lauyan Abduljabbar ya miƙe yayi suka akan wanda ya kunna Audio. Yace ai cikakken maƙiyin Abduljabbar ne, kuma computer da yazo da ita tasa ce, saboda haka basu da aminci da abinda yake kunnawa.

Alƙali da kansa ya bada amsa. “Shi fa ba shaida bane, saboda haka batun ƙiyayya (In ma akwai ta) bata taso ba. Kuma ka manta a wancan zaman kuma, naku ne yazo da tasa computer ɗin ya kunna?” Inji alƙali.

  1. Tambayoyi tsakanin lauyan gwamnati da Abduljabbar: An fara yiwa Abduljabbar Cross Examination, kuma a iyaka yau an yi masa tambayoyi 51.

Tambayoyin da aka yi wa Abduljabbar ɓangare-bangare ne. Akwai ɓangaren makarantun da ya halarta da kuma shaidun da ya samu, akwai ɓangaren malaman da yayi karatu a wajensu da kuma ijazozin da ya samu, akwai ɓangaren fannunnukan da yafi ƙwarewa a kansu, da kuma ɓangaren da aka fara tabawa, wanda ya shafi kalaman da ake tuhumar Abduljabbar a kansu.

A bisa al’adar rubutu na, ban fiye kawo tambayoyi a cikin rahoto ba, sai dai nakan ware musu rubutu na musamman, don gudun tsawaitar rahoto. Insha Allahu zan kawo muku cikakken abinda ya faru a Cross Examination daki-daki daga baya. Kuma ina tabbatar muku da cewa zaku ji abubuwan mamaki da abubuwan kunya a cikin amsoshin tambayoyin da Abduljabbar ya bayar.
Bari na baku samfurin guda biyu ko uku:

Lauya: Kana da Qualification daka samu a wata makaranta da kayi?

Abduljabbar: akwai nassin da ya wajabta sai nayi?

Lauya: Baka bani amsa ba.

Abduljabbar: Ai ni Doctoring Degree ma gareni. Kuma ina da Degree wanda Sarkin Morocco ya bani, wanda yafi Doctoring Degree. Kuma mahaifina ma ya bani shaidar ilimi tunda ya nada ni ‘Amirul Wa’izina’.

Lauya: Kenan Sarkin Morocco jami’a ce?

Abduljabbar: A’a, ba jami’a bane, amma yafi jami’a…

(Ku jira rahoto akan tambayoyi).

  1. Roƙon korar ƙara: bayan lauyan gwamnati ya tsagaita tambayoyi, ya nemi kotu ta ɗaga musu zuwa zama na gaba domin su cigaba. An tambayi lauyan Abduljabbar yana da suka? ”Bani da suka akan wannan, amma ina da roko akan wani abin daban” inji lauyan Abduljabbar.

Barista Dalhatu Shehu Usman ya roki kotu ta sallami Abduljabbar, saboda wasu dalilai nasa wanda ya zayyanawa kotu bisa fahimtar sa.

Lauyan yace: a fahimtarsa, ana zargin Abduljabbar ne da yiwa Bukhari da Muslim ƙarya, amma ba zagin Annabi SAW ba. Yace kuma dokar da lauyoyin gwamnati suka kafa hujja da ita a cikin tuhumarsu, tana magana ne akan zagin Annabi SAW ba akan yiwa Bukhari da Muslim ƙarya ba. Sannan yace: a cikin tuhuma ta huɗu, masu gabatar da ƙara a wajen gina tuhumar su, sun yi amfani ‘ma’ana’ ba da ‘lafazi’ ba a wajen cewa Abduljabbar ya yiwa Annabi SAW ƙazafin zina, saboda faɗinsa “ya bita kwararo ya biya mata buƙata irin ta ɗa namiji da mace”. Kenan don me zasu yi abinda suke tuhumarsa a kansa?

Bayan lauyan Abduljabbar ya kammala koro jawabansa. Alƙali ya bada dama ga lauyoyin gwamnati su ka yi suka sama-sama akan kalaman lauyan Abduljabbar. Daga ƙarshe alƙali yace a dakata saboda ƙurewar lokaci, amma ta kan wannan gabar za’a fara a zama na gaba.

  1. A ƙarshe alƙali ya dage shari’ar zuwa ranar 7/7/2022.

Tanbihi: Wasu suna ta yaɗa labarin cewa Abduljabbar ya fashe da kuka a gaban kotu. Wannan labarin bai faru ba. Kuma ba haka yake ba. Sai mu kiyaye.

Muna rokon Allah madaukakin Ya taimaki gaskiya da masu gaskiya, Ya kuma rusa karya da makaryata.

abduljabbar #dan_tamore #yan_kogo #shariar_abduljabbar

Awaisu Al’arabee Fagge
Director, Jibwis Social Media
Kano State.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button