Mulki dai ya kare

MULKIN DAI YA KARE
Arewa babu wutar
Mambila
Babu ruwan Baro
Babu kamfanin Ajaokuta
Babu Rijiyoyin man Fetur a Bauchi da Gombe!
Babu makarantar Petroleum Training Institute ta Kaduna!
Babu wutar Zungeru
Babu wutar Mambilla
Babu layin dogon Kano-Kaduna!
Babu layin dodon Kano-Katsina-Maradin jamhuriyar Niger
Babu na Lagos-Maiduguri!
An kasa gyaran Refineries!
An kasa gina sabbin Refineries duk da alkawarin da suka yi!
An kasa gyara sha’anin ilimi!
Kusan shekara babu karatu a jami’oin mu!
An kasa gyara sha’anin lafiya da Asibitocin Gwamnati!
A yau 12.5kg silindar gas yana farashin Naira N8000+ Gas (diesel) #790 liter!
Shan man fetur a farashin Gwamnati ya zama tashin hankali sai yadda ka samu An bada bashin noma amma ‘yan ta’adda sun hana noman
Duk inda shanu suke anbi an sace Mun koma sai mun biya ‘yan ta’adda haraji kamun su barmu mu zauna a garuruwanmu Mun koma sai mun biya ‘yan ta’adda haraji kafin su barmu muyi noma
A Arewa kowa a tsorace yake Sun mayar da ‘yan Arewa ‘yan gudun hijira a cikin Kasar su na asali saboda tsoron Kidnappers Sun mayar da hanyar Abuja zuwa Kaduna tarkon mutuwa