LABARAI/NEWS

Mun Amince Da Sake Fasalin Naira Amma Akwai Abu Ɗaya…, Inji Majalisar Sanatoci

Mun Amince Da Sake Fasalin Naira Amma Akwai Abu Ɗaya…, Inji Majalisar Sanatoci

Majalisar dattawa a ranar Laraba 16 ga watan Nuwamba ta bayyana goyon bayanta ga manufar babban Najeriya (CBN) na sake fasalin kudin Najeriya, The Nation ta ruwaito

Wannan na zuwa ne daga shawarin da majalisar ta yi ta bangaren shugaban kwamitinta kan harkokin banki, inshora da hada-hadar kudi, Sanata Sani Uba.

 

 

Yayin da ta amince da sake fasalin, ta kuma yi tsokaci da cewa, karshen watan Janairu ya yi kusa ga mayar da kudaden da ke yawo a kasar zuwa banki.

Majalisar ta yi kira ga CBN da ya yi aikin wayar da kan jama’a, musamman a yankunan karkara domin tabbatar da ‘yan Najeriya sun san da sabuwar dokar mayar da kudade banki.

Ta bayyana cewa, hakan ne zai taimakawa ‘yan Najeriya mazauna karkara su san halin da ake ciki don kaucewa tafka asara bangarensu.

Ta kuma bukaci CBN da ya tabbatar da saukaka hanyoyin hada-hadar kudi na zamani domin ba da dama ga ‘yan kasa su shigar da kudaden banki a lokacin da aka ayyana.

Hakazalika, majalisa ta nemi CBN ya tabbatar tsaron jama’ar da za su dauko kudadensu daga nesa, musamman ganin yadda ake yawan samun ta’addanci a kasar nan.

Daga karshe ta nemi bankin ya samar da hanyoyin da za su tabbatar da ‘yan ta’adda basu samu damar shigar da kudaden da ke hannunsu ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button