LABARAI/NEWS

Mun san cewa za a kai hari jirgin kasa – El-Rufa’i

Gwamnan Kaduna a Najeriya Nasir El-Rufa’i ya ce watanni biyu kenan da suka samu bayanan sirri daga jami’an tsaro cewa ana kitsa kai hari kan jirgin kasa.

Saboda duk zirga-zirga da abubuwan da ‘yan bindiga ke aikatawa ana sani, har daga inda suke komai an sani, a cewarsa.

Hatta maganganunsu ta waya, kuma an rubuta wasiƙa zuwa ga hukumar kula da sufurin jiragen kasa kan cewa a daina zirga-zirga daren amma aka ƙi.

Ya ce wasikarsu na cewa a rinƙa komai da rana saboda zai fi tsaro da sauƙi wajen kai agaji idan wani abu ya faru. Zirga-zirgar jiragen kar su ke wuce 4 na yamma.

Ya ce yana sanar da hakan ne domin mutane sun san abin da ke faruwa saboda akwai waɗanda ya kamata suyi wasu ayyukan amma sun ƙi.

Sai dai gwamnan ya ce ba za su daina matsawa shugaban ƙasa da sojoji ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button