LABARAI/NEWSFadakarwa

MUSHIRIKAN ƁOYE, MATALAUTA A QIYAMA

MUSHIRIKAN ƁOYE, MATALAUTA A QIYAMA

A lahira ko kallonsu Allah (SWT) bazai ba, alhalin sun riqa sallah, sun rika azumi, kilama har Hajji da Umrah duk sunyi… Saide gurin Allah duk na banza ne. Sun sha yunwar banza da wofi, sunyi sallar banza, sun kuma yi sadakar banza tare da Shan dadin jirgin banza da wofi.

Galibi duk sanda aka tashi bayani mafi yawan marubuta basa zancen irin wannan mutanen, saide ko yaushe atare kan yan siyasa, Yan film, mazinata da makamantansu….

Alhalin suma wadannan mutane ne da sun yawaita a wannan dandali…. kuma suna daga cikin masu jawo masifa cikin al’umma a doron kasa

Kai kusan kowama nada irinsu cikin friends dinsa, inma baka dasu toh da wuya karasa wata ko wani wanda sune sillar wargaza Wani abu nasa.

■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■

Ina magana ne akan mushirikan cikin mu… cikin Mazan mu da Matan mu; wato masu zuwa suna ma bayin Allah SIHIRI ko ASIRI, haka kurum basuji ba basu gani ba domin son ransu, domin biyan bukatar ransu.

■ Wata wacce Allah ya ɗebewa Albarkar, saboda kurum mijinta zai ƙara aure zata tashi taita fankan-fankan har sai ta sami wani kafirin Allah irinta wanda ya kwashe kayansa daga gaban manzon Allah (SAW) su shiga su fita su watsa zancen auren…. karshen mijin ya auka zinace-zinace inba Allah ya kiyaye ba.

■Wata la’ananniyar wacce ake shirin aura zataiwa asiri ta kashe kota haukata, ko lafiya taqi samuwa ajikinta

■ Wata shegiyar saima anyi auren sannan zatai asiri duk randa mijin yaje zai kusanci amaryar kode gabansa yaki tashi, ko kuma yaji amaryar na wari kamar ja6a ta gitta ta jikinta wanda hakan shi zai hanshi kusantarta

■ Wani shegen asiri yake haɗawa duk yarinyar da ya gani atiti inyaci buri sai yasan yadda yayi ya lalatata koda kuwa mutuniyar kirki…

■ Wani shegen matan aure yake bi ya riqa zuwa har gida suna cin amanar mijin… duk abunda yacewa mace bazata iya cemasa Aa’h ba

■ Wata matsiyaciyar karshenta tama fara tsufa amma haka zata shiga tsakanin danta da matansa ko matarsa, ko yayansa ta kau masa dakai akansu. Gashi da arziki amma matansa kullum a wahala da ciwo bashi sai abunda takeso zai. Kuma dan bawani bambanci yake nuna mata ba….

■ Wata shegiyar aikinta kenan tallan bokaye bata wancan gida bata wancan gida… tana hada connection

■ Wata shaidaniyar takai ga intaga mace ko wacce iri ce saita jata tai fasikancin da ita ta hanyar madigo….

■ Haka wani shegen shima shaidan ya bashi sa’a duk inda yaga wani namijin ko yaro ne sai ya lalatashi

■ Wata yar banzar yayan kishiyarta take ta sawa agaba tashiga ta fita gashi sun isa aure amma sam aga ba wanda yake zuwa neman aurensu

■ Wata shegiyar kuma itace aka auro amma da kullumboto da tashi fadi har saita fidda uwar gidan da yayanta. Ta kuma kau da kan mijin daga kansu…. ya zamto baisan ma halin da yaren suke ba

■ Wani shegen zakaga dan uwansa yakewa asiri yasa yaita masa abubuwa duk yadda yakeso! Kome ya tambayesa bazai iya cewa a’a ba saboda ya maka masa asiri ya kulle bakinsa….

■ Wani shegen bashin kaya da kudin mutane zaita kar6a kuma babu me iya tambayarsa… ya kulle bakinsu ya gama shari’a saide a kiyama

■ Wasu ko watama zasu rabaka da garinku ne baki daya… ka tafi duniya kurum kaje can ma… ko mota ta bigeka atiti, ko namun jeji su cinyeka, ko kafada wani ruwa can ka halaka, ko ka makance, kai koma de ya zamto inma kana raye toh de gudun garinku zakaita yi bama kaso wani wanda yasanka ya gansu

■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■

Ya yan uwana musulmi wadannan baki daya nau’ikan mutanen dana lissafa mutane ne da kullum muna nan tare dasu cikin mu muna rayuwa,… mutane ne da suke tafka kafirci a boye suna ganin ba wanda yasan sunayi. Basa tsoron Allah ko kadan, sannan basa jin remorse suji sun tuba sunyi nadama saboda kafirci ya shiga ransu….

Kuma suna daga cikin wadanda zakaji suna aibata wasu, koma shugabanni, sunfi kowa shiga damuwa in Allah ya jarabcesu da babu alhalin suna daga cikin masu jawo bala’I cikin alumma amma sam basa ta6a daukar abunda suke wani abu ne mai girma…

Kuma ahaka zakaji suna sallah kuma wai suna azumi. Ai wallahi inde kinsan kina daya daga cikin mutanen nan dake iya yiwa wasu asiri su rabasu da lafiya, hankali, mijinsu, ya’ya ko rayuwar ma gaba daya…. da kin ko ka dena sallarma baki daya yafi muku.

Domin ba lada🙅‍♂️ domin Allah na bada ladan ibada ne ga masu imani… kai kuwa baka da imani, domin me imani baya irin aikin da kukeyi. KUMA WALLAHI DUK WANDA YA KUSKURA MUTUWA TAZO MASA A HAKA batare da ya TUBA ya dena ba…. Wallahi bashi ba rahamar Allah, idan Kaga mutum ya shiga ALJANNA toh Allah ya FASA ƙona Fir’auna.

Amma inde fir’auna zai shiga wuta toh shima ko itama saita shiga… kuma daga sanda aka rusa kukan mutuwarki daga lokacin zaki gane wanene Allah.

Bala’in duniya da lahira a lokacin zai ƙwankwasa muku kofa.. a lokacin mutum zaiga wulakancin mutuwa, a lokacin mutum zai san menene ɗacin Mutuwa, duhu da ƙuncin kabari. Kullum bala’i yaita ƙaruwa akan mutum kenan ba ranar ƙarewa.

■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■

Haka kurum saboda kafirci ku rika mu’amala da aljanu kuna tara dukiya, tare da nakasa wasu, cinna gobara a kayan wasu, daure bakin mutane sai abunda kukeso da sauran mugayen ayyuka….

Toh wallahi muji tsoron Allah. Domin ko cikin aljanu akwai musulmai masu imani, amma ku dama da yan uwanku kafiran ake hadaku… domin aljanu mafi yawansu sun kasance masu bijirewa ne ga ubangiji bazasui ma abu ba kaima saika bijirewa Allah.

Kasani dukiyar nan da suke baka ta wani suke kwasowa. Mutane da yawa na shiga halaka adalilin neman duniyar nan wacce bakomi ba.

■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■

Da yawa kafin sukai ga samun wadannan abubuwan… wani sai aljanin ko bokan dakansa ya gidanya masai sharrudan kafirci…. Wanda kadan daga cikin hakan shine wani zaice;

● Acikin sallolin farilla guda 5 sai ka daina yin 1 aciki.

● Wani zaice kake sallah amma banda yin alwala.

● Wani zaice sai lokacin da bukatarka ta taso ka kirashi. Amma alokacin kai turare ka cire kaya ya zo ya sameka tsirara.

● Wani zaice kake komi amma ka dena wankan janaba.

● Wani kangararren aljanin zaice abunda yake bukata shine yayi luwadi dakai.

● Wani zaice sujjada yake bukata. Kaimasa duk sati sau 1 ko kullum.

● Wani zai ce bangaren jikin dan adam yake bukata; misali bangaren nonon hagu na mace budurwa yar shekara kaza…

● Ko yana bukatar jariri mace ko namiji dan wata kaza…ko kwana kaza..

● Wani ace saide ya aje alkur’ani duk sanda yai bahaya to ya yagi page guda ya katse dashi tukun. Subahanallah😥

● Wani ace saide yake zuwa yana jefa alkur’ani acikin shadda iri kaza duk sati sati ko wata..😭

● Wani suce sai ka rika kwanciya da yar cikinsa.

● Wasu ace sai sunke saduwa da matansu na aure ko kananun yara ta dubura.

● Wani suce sai ya rika luwadi da yara kuma sanda zaiyin sai ya samo alkurani yasa akasan shimfidar.

● Wani zai ce mazakutar d’a namiji yake bukata. Shyasa duk yau muke ganin balai iri iri ga mutum a mace amma kaga an kwakule idanu, nono, ds duk aljanu ne ke sawa don tsafi.

● Wata ace saita kawo gashin kan sumar mijinta, ko maniyyinsa

● Wata jinin haila za’a ce ta kawo ai rubutun sunan allah dashi a wanke abata ace taje take sama mijin a abinci yanaci… subahanallah

● Wata haka zindikin kafirin zaice saita bashi hadin kai ta sadu dashi

● Wata boka yace zai mata wanka…

Gashi nan de da abubuwa iri iri na shirka…😭😭😭

■■■■■■■■■■■■■■■■■■

Ya Allah kai mana katangar karfe dasu. Hakika yau cikin maza ko mata duk akwaisu. Wasu ma muna tare amma bamusan irin mugun aikin da suke ba, banda haka da ko inuwa mun dena hadawa dasu.

Aljanu nata jan mutane zuwa ga kafirci, saboda mutanen sun gaza sui hakuri su rayu akan yadda Allah ya ajesu cikin talauci ko wadata. Sai kadan daga cikin bayin Allah nagari.

Musulmai muji tsoron Allah! Masu wannan aiki kudena zuwa wajen yan tsubbu da yan duba. Basa amfana muku komi sai SHIRKA, kusani sanda kuka tashi kukaje da kun hakuri abunda kukagani ya faru bayan kunje din WLH zai faru koda bakuje ba.

Don haka inkinsan ko kasan kaiwa wani asiri kuma kaci karo da wannan rubutun kuima Allah kuiwa annabi kuje ku warwaresu…. ku nemi gafarar ubangiji ko kwa mutu da imani.

Muji tsoron Allah

■■■■■■■■■■■■■■■■■■
Sannan sauran al’umma mu dage da azkar, addu’oi yayin fita gida, shigowa gida, shiga bandaki, cin abinci da sauransu. Tare da yawaita sadaka domin tana maganin masifu.

Allah muke roko kasa mugama lafiya Aamin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button