ylliX - Online Advertising Network Mutane 200 sun mutu a rikici tsakanin Hausawa da ƙabila a Sudan - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Mutane 200 sun mutu a rikici tsakanin Hausawa da ƙabila a Sudan

Mutane 200 sun mutu a rikici tsakanin Hausawa da ƙabila a Sudan

Jami’ai a Sudan sun ce yawan mutanen da suka mutu a rikicin ƙabilanci da ake yi a kudancin kasar tsakanin Hausawa da ‘yan kabilar Berta ya ƙaru zuwa 200.

Wani shugaban al’umma a Jihar Blue Nile ya ce an yi kashe-kashen ne a kauyuwa uku, inda ya yi kira ga kungiyoyin agaji da su taimaka wajen binne gawarwakin wadanda suka rasu.

Rahotanni na cewa ana rikici tsakanin Hausawa da Berta ya ɓarke ne kan gonaki.

A jiya Juma’a aka sanya dokar ta-ɓaci ta tsawon kwana 30 a fadin jihar ta Blue Nile Mutum 150 ne su ka mutu a kwana biyu da ɓarkewar rikicin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button