LABARAI/NEWS

Mutane Sun Jiggata Saboda Wannan Chanjin kudin da aka sauya inda kowa ya ji a jikin da talaka da mai kudin kowa ya gane Kuren sa

Mutane Sun Jiggata Saboda Wannan Chanjin kudin da aka sauya inda kowa ya ji a jikin da talaka da mai kudin kowa ya gane Kuren sa

 

Koda yake dai Babban Bankin Najeriya ya bayyana ƙarin aƙalla ƙwanaki Goma domin karɓar tsofaffin takardun kuɗi amma dai anji jiki

 

Lamarin chanjin kuɗin nan duk da Gwamnan babban bankin ya bayyana cewa sun ga alfanun shi yadda ya kamata ya sanya kuɗaden dake hannun Mutane sun dawo cikin Bankuna da kusan kashi Tamanin cikin Ɗari yayinda suke jiran aƙalla Naira Bilyan Ɗari Tara da har yanzu ba’a dawo dasu cikin Bankuna

 

Wannan yunƙurin ya sanya ƙananan ƴan kasuwa da dama sun tsaida kasuwancin su na ƴan ƙwanaki domin gudun faɗawa asara, naga masu sana’ar abinci masu shayi da masu zuwa kasuwannin ƙauyuka da dama da suka koma suka rungume hannuwa suna jiran tsammani

 

Shawara ga Mutane Bankin dai ya bayyana cewa ya turo da Mutane na Musamman domin zuwa yankunan karkara domin chanzama Mutane Sababbin takardun kuɗin ayi ƙoƙari akai tsofaffin takardun kuɗin Inda akaga Jami’an domin a sauya da sabbin kudin

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button