LABARAI/NEWS

Mutanen Gari Sun Kori Wani Mutum Tare Da Ɗiyarsa Bayan Da Aka Lura Cewa Yana Lalata Da Ita

Mutanen Gari Sun Kori Wani Mutum Tare Da Ɗiyarsa Bayan Da Aka Lura Cewa Yana Lalata Da Ita

Jama’ar gari sun kori wani mutum daga garinsu bayan ganin yana lalata da ɗiyarsa ta cikinsa bayan an tambayeta kuma ta bayyana gaskiya, a yayin da ta ke zantawa da manema labarai

Dama tun farko an kori Amaechi Agnalasi da ɗiyarsa, Queen Bassey daga garin Nnobi da ke jihar Anambra bayan gano su na lalata da juna har sun haifi yara biyu

Ta bayyana yadda mahaifin na ta ya dinga lalata da ita kuma ya sanya ta tayi alƙawarin ba za ta sa ke kula wani ba sai shi Yayin da aka turke shi don ayi masa tambayoyi, Amaechi ya ce ya tilasta ɗiyarsa ta yi masa rantsuwa saboda ba ya so ta bar shi

Ya ce sauran yaransa sun gudu sun barshi, wannan dalilin ne yasa ya yi hakan don kada Queen ta bar shi, shi yasa ya fara lalata da ita a yanzu haka ma muna da yara biyu Yace yanzu yana kallon yaran da suka haifa ne a matsayin ƴaƴan sa kuma jikokinsa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button