ylliX - Online Advertising Network Mutum 17 sun mutu a zanga-zangar adawa da hijabi a Iran - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Mutum 17 sun mutu a zanga-zangar adawa da hijabi a Iran

Mutum 17 sun mutu a zanga-zangar adawa da hijabi a Iran

Zanga-zangar da ake yi a Iran ta fantsama zuwa birane fiye da takwas da kuma wasu garuruwa a yayin da aka shiga rana ta shida da fara ta, bayan mutuwar wata matashiya a wajen ‘yan sanda a lokacin da take tsare.

Kafar talbijin din kasar ta ce mutum 17 sun mutu ciki har da jami’an tsaro uku ne suka rasa rayukansu a yayin zanga-zangar.

A Mashhad, birni mai tsarki a Iran din, wata mata ta tsaya gaban motar ‘yan sanda tana ihu tana cewa ba ma son Jamhuriyyar Musulunci.

Rundunar juyin juya halin kasar ta yi kira ga ma’aikatar shari’a a kan ta hukunta duk masu yaɗa jita-jitar karya, sannan kuma mahukunta na kokarin rufe intanet a kasar.

Matashiyar Mahsa Amini mai kimanin shekara 22 a duniya, ta mutu ne a ranar Juma’a, kwanaki uku bayan an tsare ta a kan rashin sanya dankali yadda ya dace.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button