LABARAI/NEWS

Mutum 20 Sun Kone Kurmus Sanadiyyar Hatsarin Mota A Jihar oyo

Mutum 20 Sun Kone Kurmus Sanadiyyar Hatsarin Mota A Jihar oyo

 

Matafiya 20 ne suka kone kurmus a wani hatsari da ya ritsa da motocin haya biyu a kauyen Huturu da ke kan hanyar Oyo

 

Kwamandan Kiyaye Haddura ta Kasa FRSC Reshen Jihar oyo Yusuf Abdullahi ya ce mutanen da hatsarin ya ritsa da su yan kasuwa ne a cikin wata mota kirar Golf 3 wadda ta yi karo da wata kirar Volkswagen Sharon

 

 

Ya bayyana cewa mutum 21 ne a cikin motocin yan kasuwa wadanda 20 daga cikinsu suka rasu wani direba ya tsallake rijiya da baya Yusuf ya ce Hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce ka’ida da kokarin wuce motor dake tafiya a gaba da misalin karfe 11 safiya

 

Mutanenmu sun samu rahoton ne da misalin karfe 11:38 na safe cewa wani direba ya jikkata fasinjoji 20 sun kone kurmus maza 11 mata biyar namiji daya da yara mata uku

 

An kai direban da ya ji rauni asibitin Kafin Madaki yayin da fasinjojin da suka mutu aka binne su kauyen Huturu Yusuf ya gargadi direbobin da su guji yin gudun wuce saa tare da yin tukin mota a tsaka-tsaki don kiyaye rayuwarsu da kuma lafiyar fasinjojin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button