LABARAI/NEWS

Mutum 30 Sun Bata Bayan Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Da Rana

Mutum 30 Sun Bata Bayan Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai A Rana

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa mutane 30 sun bata, bayan wani hari da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai a ranakun karshen mako

Ganau sun shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a garin Rann lokacin da wasu mazauna garin suka tafi yin itace kuma maharan sun zo ne a kan babura

Wadanda suka tsere wa harin sun jikkata, yayin da ake fargabar maharan sun sace gwamman mutane Kawo yanzu babu tabbacin wadanda suka kai harin

sai dai dukkan mayakan Boko Haram da kungiyar IS na kai hare-hare a yankin Jami’an tsaron Najeriyar ba su ce uffan ba kan wannan harin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button