LABARAI/NEWS

Mutum aƙalla 13 aka kashe sakamakon harin da yan fashin daji suka kai a ƙauyen Karekuka na Jihar Taraba da ke tsakiyar Najeriya da tsakar ranar Juma’a

Mutum aƙalla 13 aka kashe sakamakon harin da yan fashin daji suka kai a ƙauyen Karekuka na Jihar Taraba da ke tsakiyar Najeriya da tsakar ranar Juma’a

 

 

Kazalika an jikkata mutanen da ba a san adadinsu ba a harin waɗanda ke jinya yanzu haka a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke birnin Jalingo kamar yadda kakakin ‘yan sanda na Taraba ya shaida mana

 

 

Tuni aka yi jana’izar mutanen a garin da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, akasarinsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada

 

 

 

Yan sanda sun ce tun farko mutanen garin ne suka kama ɗaya daga cikin yan fashin bayan wani hari da suka kai kuma suka kashe shi inda su kuma suka kashe mutum 13 a harin ramuwar gayya

 

 

Sai dai wasu rahotanni na cewa ‘yan bindigar sun sake yi wa Garin Gidado tsinke a safiyar yau Asabar amma sun tarar ba mutane a garin SP Abdullhi Usman ya ce an tura jami’an tsaro yankin don kwashe gawarwakin mutanen bayan harin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button