ylliX - Online Advertising Network mutumin da ya fi kowa kai kara kotu a duniya - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

mutumin da ya fi kowa kai kara kotu a duniya

MUTUMIN DA YA FI KOWA KAI KARA KOTU A DUNIYA

Duniya dai a koda yaushe tana cike da abubuwan ban mamaki da kuma ta’ajibi

A nan kuma wani mutum ne mai suna Mista Jonathan Lee Riches Wanda Aka haifa a watan Disamba 27, 1976 Philadelphia, jihar Pennsylvania A Amurka wanda ya yi kaurin suna wajen maka mutane a kotu, sakamakon wani abu da suka yi masa; ciki kuwa da har mahaifiyar da haife shi

Jonathan har mahaifiyarsa ya shigar da kara a Kotu, inda ya fada wa kotu cewa, mahaifiyar tasa ba ta ba shi kulawa yadda ya kamata ba, wanda a karshe dai Mista Jonathan ya samu nasara a kan mahaifiyar tasa, inda kotu ta umarce ta da ta biya shi kudi Dala $20,000

Bayan wannan nasara da ya yi Mista Jonathan ya sake shigar da amininsa da makocinsa da wasu daga cikin ‘yan uwansa har da ma budurwarsa da kuma wasu ‘ yan sanda, sannan ya shigar da karar wani

Hakazalika, ya maka wani kamfani a kotu da tsohon shugaban Kasar Amuruka, George Bush, kuma duk ya samu nasara a kan kowace kara da kai kotu

Tun 8 ga Janairu, 2006, ya shigar da kararraki sama da 2600 a kotunan gundumomi na tarayya a duk fadin kasar, wasu daga cikinsu sun sami kulawar manema labarai sosai

Daga baya A Shekarar 2009 an sa sunan Mista Jonathan Lee a matsayin wanda ya fi kowa shigar da kara a kundin tarihi na duniya (World Guinness Book Record), wanda ganin sunansa a cikin wannan kundi ya sa Mista Jonathan ya shigar da karar Guinness Book of Record gaban kotu bisa rubuta rayuwarsa a cikin kundin ba tare sahalewar sa ba. Ya kuma samu nasara a kotun da kudi har Dala $8,000.000

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button