LABARAI/NEWS

Na Bai Wa Lauya N2m Ya Kai Wa Alkali Don A Sake Ni —Abduljabbar

Na Bai Wa Lauya N2m Ya Kai Wa Alkali Don A Sake Ni —Abduljabbar

Fitaccen malamin nan da gwamnatin Kano ta gurfanar a kotu kan zargin batanci ga Annabi, Sheikh Abduljabbar Sheikh Naziru kabara yayi zargin lauyan sa Dalhatu Shehu Usman da karbar cin hanci daga hannun sa, da nufin cewa Alkali ne yace abashi kudin da ya wanke shi a fito dashi daga Gidan Yari

Abduljabbar Nasiru kabara yace an bawa Alkali kudi N1.3m, shi kuma Lauyan sa Dalhatu Shehu Usman ya tashi da N500,000 Amma shi lauyan Abduljabbar Nasiru kabara, Dalhatu Shehu Usman da Alkali Sarki Yola sun ce wannan maganar ba gaskiya bane karya ne

Inda shi lauyan harya Kara da cewa acikin su ma akwai wadanda shi Abduljabbar Nasiru kabara din seda ya zarge su da Neman Matarsa
Abduljabbar Nasiru kabara yakara da cewa, Lauya sa Dalhatu Shehu Usman Shine yazo har Gidan Yarin ya same shi yafada masa cewa Alkali Sarki Yola ya umarce Shi dayazo yagaya masa ya biya Naira Miliyan biyu 2 za a zo a wanke shi

Yace kuma Lauyan ya tabbatar masa da cewa yabawa Alkali Sarki Yola N1.3m, sannan yaba wani Mutum N200,000, shi kuma a karan kansa lauyan ya dauki N500,000

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button