ylliX - Online Advertising Network Na faɗawa Sarki Charles III cewa bani da gidan kai na a Landan, ~ Cewar Shugaba Buhari - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Na faɗawa Sarki Charles III cewa bani da gidan kai na a Landan, ~ Cewar Shugaba Buhari

Na faɗawa Sarki Charles III cewa bani da gidan kai na a Landan, ~ Cewar Shugaba Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce a lokacin ganawa da Sarki Charles na III, a fadar Buckingham ya shaida masa cewa ba shi da gida kan sa a Burtaniya.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin ganawa da ‘yan jarida bayan ganawa da sarkin mai shekara 73,

 

 

Buhari ya ce sarkin ya tambaye shi ne ko yana da gidan kansa a Burtaniya Buhari ya ce makusudin ziyara ita ce tattaunawa kan alaka tsakanin kasashen biyu ta fuskar kasuwanci da diflomasiyya.

Ya ce an tsara ganawar ta su ce a baya a Kigali tun kafin ya zama sarki, sai dai a wannan lokaci ne ganawar ta tabbata.

Wannan ce ganawa ta farko tsakanin shugaba Buhari da basaraken tun bayan hawan sa kan karagar mulki.

Bayanai na cewa ganawar ta bai wa shugaban na Najeriya damar taya sarkin murnar hawa mulki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button