LABARAI/NEWS

Na Fi Son Kashe Mutane Fiye Da Yin Garkuwa Da Su, Cewar Ado Alero dan Ta’addan Da Aka Baiwa Sarauta A Zamfara

Na Fi Son Kashe Mutane Fiye Da Yin Garkuwa Da Su, Cewar Ado Alero dan Ta’addan Da Aka Baiwa Sarauta A Zamfara

Rariya ta ruwaito rahoton yadda Gawurtaccen dan fashin dajin nan da aka nada matsayin Sabon Sarkin Fulanin Ƴandoton Daji jihar Zamfara Ado Alero yace ba ya da burin garkuwa da mutane, yafi son ya kashe su kawai.

Ado aleru ya bayyana cewa yafi Son Kashe Mutane Fiye Da Yin Garkuwa Da Su, Ado alero dai dan ta’adda ne daya takurawa jahar katsina da zamfara hakan yasa har yau Hukumar yan sandan jahar katsina take neman sa ruwa a jallo.

Alero yace abin dake ci musu tuwo a kwarya shi ne yadda Hausawa suka cinye labi-labi da burtullan da Fulani ke kiwo, ta yadda dangantaka ta yi tsami tsakanin bangarorin biyu.

Nadin Ado Alero dai ya jaza gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin ‘Yandoton Daji da ke yankin karamar hukumar Tsafe ta jihar.Related

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button