ylliX - Online Advertising Network Na Sami Mijin Aure A Na Facebook Ina Yiwa Wanda Yace Yana Ƙaunata Fatan Alkhairi Cewar Moofy - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Na Sami Mijin Aure A Na Facebook Ina Yiwa Wanda Yace Yana Ƙaunata Fatan Alkhairi Cewar Moofy

Na Sami Mijin Aure A Facebook Ina Yiwa Wanda Yace Yana Ƙaunata Fatan Alkhairi Cewar Moofy

Fitacciyar mawaƙiyar nan mai suna Mufeeda Adnan da aka fi sani da Moofy mai fassara a Kanfanin Algaita ta bayyana jin dadin ta game da yadda wani matashi ya nuna ƙauna a gare ta.

Jaridar Amintacciya ta wallafa wani labari wanda wani matashi mai suna Al-Mubarak Yakubu Muhammad dan jihar Kano ya bayyana cewa, tunda daɗewa ya kamu da kaunar Mawakiyar.

A cewar matashin yana so idan taga saƙon sa ta sani yana ƙaunar ta da Aure wallahi A karshe matashin ya bada lambar sa inda ya nemi data tuntube shi saboda bai san yadda zai haɗu da ita ba

Sai dai bayan mawakiyar taga saƙon ta bayyana jin dadin ta, inda ta rubuta kamar haka Allah Sarki Nagode Allah ya saka da alheri. Watanni uku da suka wuce na samu mijin aure kuma daga Facebook ina maka fatan alheri tare da addu’a Allah Ubangiji ya baka wacce ta fini ta ko ina I Love your courage and confidence Wallahi. Zan kiraka insha Allah mu gaisa Al-mubarak inji Moofy

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button