Islamic Chemist

AMFANIN NA’A-NA’A GA KAJI

MAGANI A GONAR YARO Kashi na 12
NA’A-NA’A GA MASU KIWON KAJI
Barkanmu da warhaka, ayau zamu fadi yacce na’a na’a take da tasiri a gurin masu kiwon kaji. Ita wannan ciyawa nada matukar amfani a wurin kaji, sahihiyar maganin kwari ce wajen hanasu zuwa inda kaji suke indai ana saka musu dayen gayenta ko bishiyarta a wajen kwancinsu ko gurbinsu, tana kuma hana jaba da jinsinta zuwa inda suke sannan dadi da kari idanma kaji sunci tana kara musu lafiya da kuma sauke musu zafin jiki kamar a lokacin zafi sanda zakaji kaza kamar kana kuna wuta a jikinta.
Wannan yana da tasiri musamman masu kiwon maja da kajin gida domin Sufi barin kaji a gurbi su dade. Suma sauran zaka iya saka musu ita akusa dasu a dunga zuba musu gayen a ruwansu domin kara musu lafiya da kuzari.
Tura zuwa abokai da yanuwa masu kiwo don maganin jaba da beraye masu cinye musu yan tsaki, shan kwai da korar kwari masu damun kaji.
Naku
Amiru Waziri

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button