Videos

Nafisa Abdullahi da fati washa na rigima kan labarina

Nafisa Abdullahi da fati washa na rigima kan labarina

Wannan rigimar har yanzu taki lafawa wacce a ƙalla ta kusa daukar wata uku anayinta kuma ba wani abu ne ya kunna taba illa akan wani shiri mai nisan zango wato labarina wanda aka maye gurbin daya daga cikin jaruman da daya wanda hakan ya haddasa wutar gaba a tsakaninsu

Fati washa wacce kowa yasan cewa batafiya shiga cikin irin wa’yannan rigima ba sai gashi a wannan karan anjita har tana iya mayar da martani akan wannan fadan domin abin yayi matukar bata mata rai ganin yadda bata da laifi akan abun amma kuma zagi ya hau kanta

Ita dai nafisa Abdullahi ita ake ganin tafi kowa laifi akan wannan fadan domin tunda aka cireta daga shirin aka jiyota tana fadar wasu bakaken maganganu daga kan daraktoci harsu kansu wa’yanda suke taka rawar gani a wannan shirin

Ta bangaren Mutanen gari kuwa suna goyon bayan jaruma fati washa domin ana gani kamar ita har yau bata fita fadar bakar magana ba akan daya abokiyar fadan tata wanda ada itama ana yabon bata saka baki akan Komai sai yanzu dataga daukaka tazo mata sai ta fara wasu abubuwa wanda ake ganin kamar ba girmanta bane

Mudai fatan mu shine Allah ya dakatar da wannan rigimar ya kuma shirya wa’yannan jaruman guda biyu su dawo kamar da yadda suke

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button