ylliX - Online Advertising Network Najeriya ba za ta taba shiga matsalar abinci ba –Cewar Ministan Noma - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Najeriya ba za ta taba shiga matsalar abinci ba –Cewar Ministan Noma

Najeriya ba za ta taba shiga matsalar abinci ba –Cewar Ministan Noma

“Ministan noma da raya karkara, Mohammed Abubakar, ya yi watsi da fargabar da ake yi na cewa za a fuskanci karancin abinci cikin watanni masu zuwa a Najeriya.

“Yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan majalisa a wajen kare kasafin kudin hukumarsa a zauren majalisar dokokin, ministan ya ce, ba za su bari hakan ta faru ba. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na (NAN) ya ruwaito.

“Wasu daga cikin ‘yan majalisar dai sun bayyana cewa, matsalar ambaliyar ruwa za ta shafi fannin noma a kasar.

“Sun kara da cewa, an yi hasashen cewar, kasashen Afirka za su fuskanci karancin abinci sakamakon rashin shigo da abinci da yakin Ukraine ya haddasa.

“Ya ce ”Ba za mu bari matsalar karancin abinci ta yi tasiri a Najeriya ba, ina mai tabbatar muku da cewa da yardar Allah hakan ba za ta faru ba, saboda akwai matakai da dama da muka dauka domin magance wannan matsalar”.

“Ya ci gaba da cewa ”Daya daga cikin matakan da muka dauka shi ne noman rani, wanda muka ware masa kudi, muna aiki da ma’aikatar kudi, muna kuma samun tallafi daga cibiyoyin kudi, kamar bankin raya kasashen Afirka, dan haka za mu fadada noman ranin”.

“Ministan ya kuma ce, gwamnati na nazari kan irin barnar da ambaliyar ta haifar wa amfanin gona kamar shinkafa da masara, da kuma yawan manoman da lamarin ya shafa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button