LABARAI/NEWS

Najeriya: ‘Yan bindiga sun bi gida-gida sun yi awon gaba da mutane 36 a Kaduna

Najeriya: ‘Yan bindiga sun bi gida-gida sun yi awon gaba da mutane 36 a Kaduna

Kimanin mazauna unguwar Keke B dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna ta Najeriya 36 ne ‘yan bindiga suka sace su a Litinin.

Kimanin mazauna unguwar Keke B dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna ta Najeriya 36 ne ‘yan bindiga suka sace su a Litinin.

Rahotanni sun ce lamarin ya auku ne a yayin da yawancin mazauna yankin ke kokarin kwanta bacci a daren Litinin.

Wani ganau ya ce ‘yan bindigar, wadanda suka gudanar da aikinsu ba tare da wani ya kalubalance su ba, sun bi gida-gida suna daukar wadanda suka ga dama.

Jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun zo ne da yawa, da misalin karfe 8 da rabi na dare, dauke da bindigogi, kuma suna ta harbi kan mai uwa da wabi.

Sun yi ta fasa gidaje daya bayan daya suna dibar mutane, a cewar wani wanda ya tsallake rijiya da baya.

Babu wani bayani a hukumance daga hukumomin tsaron jihar a game da wannan lamari ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, kuma kokarin tuntubar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar kaduna ya ci tura. Sai dai rahotanni sun ce an jibge ‘yan sanda a unguwar a halin da ake ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button