Girki Adon Uwargida

NASIHA GGA MATA

Sai kaga katuwar budurwa tayi aure amma bata tsaida Sallah ba, azumi In tasha bata ramuwa sannan ko wankan haila bata iya ba balle na janaba balle wani na biki.

Haka shima “Gauden” naku Saurayi yayi Aure ka ganshi kamar mai hankali amma wlh bai san yadda ake tsarkin Fitsari bama bare hukunce hukuncen addini.

Shi jahili itama jahila babu wanda zai tada wani, bare ayi maganar addu’ar da zaiyi mata domin samun zuri’a masu anfani bai sani ba, haka zai farmata kamar balagaggen jaki in da rabo haka zasu haifo mana shaidani cikin Al umma.

Anata maganar mace macen aure, mutane nawa ne ke rayuwar auren yadda Manzon Allah s.a.w) Ya nusar damu? Komai a jahilce, mu natsu musan addini munki.

Duk inda ka juya banda zawarawa babu abun da zaka kirga, auren kanta ba abi ta tafarkin addini sai dai dawata manufar ta daban. Kaje ka aje mace amma cikinku babu wanda yasan menene hakkin dayan akansa, kuwai rayuwar ake kamar tumakai. Allah kyau.

A gaskiya ya kamata mu gyara musan inda muka dosa a rayuwa ko Allah Zai kawo mamu dauki acikin lamuran mu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button