Nasir El-Rufai: Mun gaza a matsayinmu na shugabanni a Najeriya

Nasir El-Rufai: Mun gaza a matsayinmu na shugabanni a Najeriya
“Ina tsoron ranar da zan tsaya a gaban Allah na faɗi me na yi, me zan iya cewa mun yi? Saboda haka dole mu roƙi gafararku da afuwarku domin a gwamnatance mu muka kasa,” in ji Malam Nasiru.
Gwamna Elrufai ya ce ganin tasanin tashin hankali da ƙaruwar hare-haren nan akwai lokacin da ya ba da shawarar cewa a shiga dazuzzuka da suka kasance maboyar wadannan ‘yan ta’adda a ƙona su da kauyuka da dazukan baki daya.
Amma a cewar gwamnan bai samu goyon-baya ba saboda sojoji na cewa ai tun da ba yaƙi ake yi ba, idan har suka aikata hakan to nan gaba suna iya fuskatar matsala.
Gwamnan ya ce sojoji sun ba da hujjar cewa su tsoronsu shi ne nan gaba ana iya kama su idan suka bar aiki suka fita ƙetare a gurfanar da su kan laifin aikata laifukan yaƙi ko kashe fararen-hula.
Ya nuna takaicinsa kan yadda masu kashe waɗannan mutanen ba a ganin laifinsu, dai dai ya ce tun lokacin da kotu ta amince a ayyanasu a matsayin ‘yan ta’adda suke ta matsa ƙaimi kan a ƙona dazukan, amma an ƙi sauraronsu.
-BBC