Fadakarwa

Nauikan cutar Cancer da Alamomin su

KU JI SANNAN KUMA KU ILMANTU akan Nauikan cutar Cancer da Alamomin su
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

 1. Kansar nono (Breast cancer)
 2. Kansar Huhu (lung cancer)
 3. Kansar Bakin mahaifa (cervical cancer)
 4. Kansar maƙogoron mazaƙuta (Prostate cancer)
 5. Kansar hanji da dubura (colorectal cancer)

Wadannan sune cuttukan cancer guda biyar da suke kan ganiyarsu wato top5 a Nigeria wajen addaba tare da kashe mutane.

Saide na zaɓi guda daya ciki domin haska muna hanya wato KANSAR BAKIN MAHAIFA (Cervical cancer) ganin yadda take yaduwa batare da da yawa cikin mata sunsan suna dauke da ita ba Har sai tai warwatsu ta yaɗu zuwa wani sassan na jiki da yake ƙalau ada sannan agano Mace na dauke da cancer walau hantarta, huhu, hanji ko baki alhalin asalin cancer din daga mara ta taso rahin sani ne kurum….

Musamman ina tura wannan sakon ne a sirrance ga matan dasu suka fi shiga wannan hatsarin. Wato mata masu abokan saduwa fiye da ɗaya, walau cin amanar aure ko kuma budurwar dake bin samari.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Ga duk wacce tasan tana da abokanan saduwa barkatai walau budurwa, bazawara ko mai auren da bata dauki keta hakin aure komi ba…., ko kuma wacce tasan mijinta manemin matane….

Da kuma Namiji me saduwa da Mata barkatai, da kuma namiji me haikewa namiji ta dubura wato homosexuality

=> Hakika wadannan rukunin mutane sune kangaba cikin wadanda ake samu da wannan larura.

A namiji shi yana iya haduwa da kansar azzakari ne (Penile cancer).

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

MEKE FARUWA

Human papillomavirus wannan wani hatsabibin virus ne dake rikida ya haddasa cutar cancer ga duk wanda ya kama shine ke haddasa wasu alamomi da awasu matan ko maza masu abokanan saduwa barkatai ke ganin wasu kuraje marasa zafi… masu tauri kuma ba ruwa suke ja ba… wani lokacin yan faffada haka zaka gansu kamar yadda kuke gani ahotunan kasa dana sa……

Saboda basu da zafi wasu basu cika damuwa su fahimci ko menene ba.. sai ahankali sukan kara yawa su kara girma ta yadda sukan baibaye azzakarin namiji haka su kusa cikin farjin mace duk su 6atashi…. wanda ko kallo kayi bazakaso ka kara gani ba….

Haka kuma kurajen sukan yadu suzo su dabaibaye duburar mutum… nan ma su kude ciki….

A nan ne in namiji ya kamu da Hpv din tunda galibi bai sani ba tunda ba lokaci daya zaiga alamun ba…. inyazo ya sadu da mace koda so dayane shikenan ya goga mata masifa…. walau munin kurajen koda bazasu zama cancer ba abun tashin hankali ne.

Haka idan macen ce me cin amanar aure ce intaje ta kwaso ajikin wani ƙazamin in Mijinta na sunna yazo ya kusanceta shima sai ya dauka….

Ballantana uwa uba masu saduwa ta dubura wato homosexuality wannan hatta HIV tafi saurin kamasu dama… to suma zasu iya haduwa da cancer ta dubura ko colorectal cancer duk a dalilin Hpv

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

WADANNE ALAMU MACE ZATA GANI IDAN TA KAMU DA WANNAN CANCER DIN

 1. Ganin jini na dan fito ko light bleeding a tsakankanin haila… wato kafin ainshin kwanakin suyi.
 2. Ganin jinin haila na fita da yawa heavy tare kuma da wuce kwanakin da mace ta saba tanayi… wato fiye da kwana 5
 3. Mace ta rika ganin jini bayan kammala jima’i
 4. Ganin fitar farin ruwa sosai musamman hade da smells mara dadi
 5. Jin zafi yayin saduwa
 6. Ga wacce ta wuce shekarun haila bayan tsayawar hailar amma taga kuma tana ganin wani jini data rasa kansa
 7. Cigaba da Fuskantar ciwon kugu ko baya wanda anrasa dalilin sa musamman a lokutan da bana haila ba kullum kullum

Wadannan sune alamomin kansar bakin mahaifa… amma wasu matsalolin ma ka iya janyo makamantan abubuwa irin haka….. amma binkice ne kurum zai bambanta… ya kuma tabbatar.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

TA YA AKE GANE AN KAMU

A dalilin irin wadannan abubuwa ne akeson mata su daure musamman wadanda suka san sun auko rukunin wadanda nai bayani abaya cewa duk shekara su rika zuwa check up ana musu PAP SMEARS Test… wato inda likita ke amfani da strip ya shafo sample din fluids din dake bakin mahaifar mace ya aike dashi laboratory domin binkice … a tabbatar da cewa lafiya kalau take ko kuwa tana dauke da wannan Human papillomavirus din….

Don haka duk mace ma baki daya akwai bukatar take samun wannan gwajin domin zai taimaka agano abubuwa da yawa tun kafin sui muni

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

WANI ABUN DADI KUMA

Shine shi wannan virus na Human papillomavirus ana iya yin rigakafinsa…

Ga Mace intakai shekara 11 da kuma namiji inyakai shekara 12 a duniya…. ba’a yiwa yankasa da haka saide in anyiwa mace fyade a inda ake tunanin lallai zata iya kamuwa da Virus din amma ko shi sai inta shekara 9…..

Ga wadanda suke cikin shekaru kasa da ashirin wato Mata da Maza…. ana yi musu rigakafin ne sau 2 kacal. Tsakanin ta farko data biyu tazarar wata 5 ne.

Idan kuwa sunba shekaru 20 baya toh sai sun kar6i dosage 3 a maimakon biyu cikin watanni 6.

Kunga kenan kusan kowa ma yana bukatar wannan rigakafin… wanda kuma da yawa basu san hakan ba.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Don haka inbaki yadda da kanki ba… ko kina kokonto kansa… toh ki daure kije ki sami babban likita ya turaki gwajin kuma ki magana aimiki rigakafin… in akai haka toh antsallake… amma duk da haka a kauracewa abokan saduwa barkatai….

Domin koda anyi rigakafin kusani HPV kuka sami kariya amma still zaku iya haduwa da cervical cancer in mutum bai lura da kanshi ba.

Ina tabbatar muku da yanzu akwai hatsabiban cuttuka da sunsha kan Hiv wajen wulakanta lfy.

Fatan bayanin ya ilmantar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button