LABARAI/NEWS

NDLEA ta kama Kwayoyin Turamol masu yawan gaske a filin jirgin sama

NDLEA ta kama Kwayoyin Turamol masu yawan gaske a filin jirgin sama

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, sun damke magungunan da suka kai sama da Naira miliyan 2.4 mai nauyin kilogiram 2,356 a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a ranar Lahadi.

Magungunan da suka shigo kasar daga birnin Karachi na kasar Pakistan ta hanyar jirgin saman kasar Habasha sun hada da kwali bakwai na 250mg na wani iri mai suna tamral da kuma katon 45 na kwayoyin 225mg da aka yiwa lakabin fatauci

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button