Islamic Chemist

NEMAN AURE

NEMAN AURE.

(DAGA LITTAFIN KIMIYYAR AURE NA DAURAWA)

Zaɓin abokin zama a aure yafi kowane zaɓe wahala da haɗari, domin idan mutum ya tafka kuskure, ko yabi son zuciya, to ya shiga matsala kenan har ƙarshen rayuwar sa, shi ya sa ake buƙatar ilmi da wayewa da bi a sannu kafin yanke shawarar fitar da abokin rayuwar aure, saboda kusanci da sirrin da ke tsakanin mace da mijin ta.

Alaƙa tsakanin mace da namiji alaƙa ce mai tushe, Allah ta’ala ya gaya mana matakai uku a cikin ayar farko ta suratun nisai, na daya, ya halicci ƳanAdam daga Adam As, mataki na biyu ya halicci matar sa daga gare shi, na uku daga gare su ya Samar da dukkan Maza da mata, don haka soyayya da kauna da bege da shauƙi da ke tsakanin su na reshe ne da tushe, ance saboda sanin asali yasa Kare ya ci alli.
Don haka mace ta na buƙatar namiji kamar yadda namiji yake buƙatar mace, kowanne yana da abinda ɗayan bashi da shi, wanda kamalarsa da mutuntakar sa, da buƙatar sa ta jingina ga abokin tarayyar sa.

Aure abu ne mai mahimmanci a rayuwa kuma wani babban cangi ne a rayuwar mutum, idan ya yi kuskure ko ganganci, ya lalatawa kansa wani ɓangare mai girma na rayuwar sa don haka a nutsu sosai a bi ƙaida domin kaucewa nadama
Zuwa zance ko ganin mace domin gabatar mata da kai, a matsayin mai neman aure, shi ne abin da malamai suke kira neman aure ko kuma kiɗbah, asali ana neman auran mace a wajan waliyinta a mataki na farko domin samun iznin ganin ta da tattaunawa da ita, don samun fahimta, kamar yadda Manzon Allah saw ya nemi auran Aisha a wajan mahaifinta Abubakar. Bukhari 5081.

Mataki na biyu, ana iya neman auran mace kai tsaye a wajan ta idan mai hankali ce, kamar yadda Annabi saw ya nemi auran Ummu Salamata a wajan ta, har ta bayar da uzrin yawan ƴaƴa da shekaru da tsananin kishi, ya bata amsa da zai riƙe mata ƴaƴan, shekaru kuma shima yana da su, kishin kuma zai roƙi Allah ya rage mata shi, Muslim Annasa’iy.

Mataki na uku Mahaifin mace ko waliyinta zai iya gabatar da ita ga mutanan kirki, domin sama mata miji, kamar yadda S. Umar ya gabatar da Ƴarsa Hafsah ga S. Abubukar, sannan Usman daga baya Manzon Allah saw ya aure ta. Bukhari 5122. Da hadisin Umma Habibah da ta nemi Manzon Allah saw ya auri ƴar’uwarta, ya nuna mata baya hallata a musulunci haɗa ƴan’uwa a igiyar aure ɗaya a lokaci ɗaya. Bukhari 5107.
Mataki na hudu ya halatta mace mai hankali ta gabatar da kanta da wani mutum nagari ko zai amince ya aure ta, kamar yadda wata mata ta gabatar da kanta ga Manzon Allah saw, ko zai amince ya aure ta, Bukhari 5120.
Mataki na hudu wani ya na iya zama sila ko dalili wajan shige wa gaba wajan kulla alaƙar aure tsakanin masu neman aure kamar yadda kaulatu Bnt Hakeem ta gabatarwa da Manzon Allah saw auran Nana Saudah bayan wafatin mijinta.

Mataki na biyar za a iya kafa wata ƙungiya mai ɗauke da amintattun mutane masu ilimi da sanin haliyyar jama’a, su ɗinka zama masu dalilin aure, duk mai neman aure mace ko namiji sai ya je gurinsu, domin tantancewa da shigewa gaba wajan haɗa aure.

Mataki na shida za a iya buɗe wata kafa a Internet a buɗe Web site, domin wannan aiki amma yana buƙatar aiki da saka ƙaidoji domin ka da a canga munufar buɗewar zuwa wani abu daban.

HUKUNCIN BAYAR DA SHEDA AKAN MAI NEMAN AURE

Idan mutum yana neman aure amma yana da wata matsala, wacce waliyan matar ba su sani ba, ko kuma matar ta na da wata matsala amma shi mai neman aure bai sani ba, shin ya hallata wani da yasan wannan matsala ya je ya bayyana ko kuwa? Ko sai ya jira sai an tambaye shi,? Duk wannan malamai sun tattauna gwargwadon hujjoji da suke riƙe da su akan wannan mas’ala, wasu daga ciki suna ganin wajibi ne idan an tambaye ka ka faɗi gaskiya kuma kayi adalci,”IDAN ZA FAƊI MAGANA KUYI ADALCI” amma idan ba a tambaye ka ba kuma, matsalar babba ce, kamar kafurci da shirka da kungiyar matsafa, da wata mummunar bidi’a, ko wani babban fasiƙanci kamar liwadi da zina da shan giya, wannan ko ba a tambaye ka ba wajibi ka sanar da iyayan ba tare da ka bayyana musu kanka ba, kamar ka kira su ka ɓoye number ka, ka ce ya kamata su yi bincike domin akwai zargin wanda yake naman auran ƴarsu ya na aikata ɓarna iri Kaza, idan kayi haka ka sauke nauyi, su kuma ya rage nasu su bincike shi ko su yi suna sane,.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button