ylliX - Online Advertising Network Ni Ban Jefi Murtala Sule Garo Da Kofin Shayi Ba, Yana Cikin Zagi Na Ne Ya Zame Ya Faɗi Ya Fasa Baki ~ Doguwa - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Ni Ban Jefi Murtala Sule Garo Da Kofin Shayi Ba, Yana Cikin Zagi Na Ne Ya Zame Ya Faɗi Ya Fasa Baki ~ Doguwa

Ni Ban Jefi Murtala Sule Garo Da Kofin Shayi Ba, Yana Cikin Zagi Na Ne Ya Zame Ya Faɗi Ya Fasa Baki ~ Doguwa

A jiya ne dai sa’insa da ka-ce-na-cen ta ɓarke ne lokacin da shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Najeriya Honorabul Doguwa ya je gidan mataimakin gwamnan Kano a ranar Litinin.

Bayan faduwar lamarin magoya bayan Garo sun zargi doguwa da tada hayaniya, wanda Rahotanni ma sunce saida Doguwan ya Jefi Garo da kofin shayi.

A zantawar Hon Doguwa da BBC Hausa ya musanya jifan Doguwa ya bayyana cewa ko da ya isa wurin sai ya tarar ana wata ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.

Kuma a cewarsa da ya tambayi abin da yasa ba a gayyace su ba, sai ya ce an mayar masa da kakkausar amsa Tambayar kawai da na yi ita ce, ‘yanzu ya mai girma mataimakin gwamna ya kamata a ce ana taro irin wannan, ga ɓangaren gwamnati ga kwamishinoni ga ɓangaren majalisar jiha, amma mu da muke majalisar tarayya ba a gayyaci kowa daga cikinmu ba, laifin me muka yi?

Daga faɗar hakan sai kawai yaron nan Murtala yana zaune ya ce ba za a gayyace ku ɗin ba. Waɗannan kalmomi su suka hassala ni.

A wajen taron kuma a garin yana masifa yana zagina sai ya kifar da wani kofin shayi mai ruwa a ciki, sai santsi ya kwashe shi ya faɗi ya fasa bakinsa Amma sai na ji ana ta yaɗa wani zance wan na jefe shi na ji masa rauni,” in ji Doguwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button