NIGER π³πͺYAN NIGER na cigaba da rera wakokin martani ga wani malami

Niger π³πͺ yan Niger na cigaba da rare wakokin martani ga malamin da yai kalaman tsana ga yan Niger
Ashe dai har yanzu tsugunne bata kareba akan wannan malamin wanda yayi wasu kalamai ga yan Niger wanda hakan kuma ya fusata samari da yan matan kasar ta Niger wajen yi masa mummunan martani da kuma ja masa kunne
A tun kwanakin baya wani malami acikin karatu yayi wata magana wacce batayiwa yan Niger dadi ba kuma hakan yasa rigima na shirin kwarewa tsakanin samari da yan matan kasar domin ganin sun mayarawa da wannan makamin martani kuma a yanzu haka malamin ya rasa inda zai sa kansa domin irin zagin da take sha da wajen mutanen kasar
To mudai namu shine yayyafawa wannan rigimar ruwa bawai mu kara angizota ba kuma domin kuma kunsan Bama daga cikin masu karawa rugima gishiri domin mu nishadantar daku muna fatan zakuyi mana fatan alkhairi kasancewar kawo muku sahihancin labari da muka fi mayar da hankali akai
Abu sai ta azara yake amma manyan mahukunta sunki suyi Wani abu akai wasu na ganin wannan manhaja ta tiktok na karamin rigima take haddasa wa ba acikin al’umma a kullum sai kaji wata sabuwar rigima ta Kunno Kai a tsakanin wasu
Wa’yannan dai habaice habaice da yan mata da samari suke rerawa cikin waka yasa hankalin mutane gaba daya ya karkata agaresu domin abin yana matukar bayar da mamaki daga tabaku sai ku mayar da abu kamar yaki