Latest Hausa Novels

Nigeria da Nijar

Nigeria da Nijar

Posting No 22

A arewacin Nigeria, kusan kowane yaro ko yarinyar dake ɓangaren kimiyya a sakandare in ka tambaye su me kuke so ku zama za su ce maka likita. Kar ka damu da zancen da za su gaya maka na cewa wai suna so ne su zama likitoci don su taimaki ƴan uwansu mata da ƴan uwansu musulmi. Duk wannan labari ne irin wanda ake cewa a story for another day.

Now, duk da yawan jami’o’in Nigeria waɗanda ke koyar da aikin likita ba su iya biyan buƙatun rabin-rabin masu buƙatar samun gurbin karatun likitan. A jami’a kamar ABU Zaria za ka iya ganin mutum sama da 10,000 sun nemi gurbin karatun likita yayin da jami’ar ba ta iya ɗaukan ɗalibi fiye da 200 a wannan fanni.

Wannan ya sa za ka ga duk wanda ya sami admission ɗin MBBS ana ta masa murya shi da iyayensa da danginsa ana masa kallon mutumin da ya tsallake siraɗi.

Su kuwa a Nijar ba su da irin wannan tunanin, ba sa ganin likita a matsayin wani super human ko wani ɗan baiwa mai sa’a a rayuwa wanda ya cancanci a yi masa murna ko hassada. Ƴan takardarsu ba sa gogoriyo wajen neman admission zuwa faculty of medicine. Tare da cewa ba su da yawan makarantu irin namu waɗanda ke karantar da likitanci. Amma a jami’ar gwamnati ta Niamey kawai akwai gurbin karatun likita na kimanin mutum 500. Kuma ana iya samun masu son karanta likitancin gwargwadon buƙata a duk shekara. Amma galibin ɗalibai ba sa son MBBS. Saboda daɗewar karatun (shekara 8 shine mafi ƙaranci) Sannan kuma kana iya gamawa ka rasa gurbin aiki tamkar wanda ya karanta Arabic ko Archaeology ko Education ko Library Science ko Zoology ko duk wani course da ƴan Nigeria ke karantawa in sun rasa Medicine da Pharmacy da Nursing da Law da Bus. Admin da Architecture da sauran kwasa-kwasai masu farin jini.

Sai dai kuma a yanzu akwai jami’o’i masu zaman kansu da suka fara yawaita a cikin jamhuriyar Nijar ɗin, cikinsu har da masu karantarwa da Ingilishi, waɗanda abin mamaki, galibinsu mallakar ƴan Nigeria ne kuma cike suke da ɗalibai ƴan Nigeria. Ka san mu ƴan Nigeria we are known to be crazy about anything foreign.

Mu kwana lafiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button