LABARAI/NEWS

NIGERIA TA SAMU LASISIN FARA AMFANI DA JIRGIN YAKI MAFI HATSARI GA ‘YAN TA’ADDA

NIGERIA TA SAMU LASISIN FARA AMFANI DA JIRGIN YAKI MAFI HATSARI GA ‘YAN TA’ADDA

Labarai mai dadin ji garemu ‘yan Nigeria, Maigirma Ministan shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin tarayyar Nigeria Barr. Abubakar Malami, SAN yau talata 4-1-2022 a hiran da akayi dashi a NTA cikin shirin “Good Morning Nigeria” ya bayyana cewa Gwamnatin Nigeria ta samu lasisin fara amfani da jiragen yaki mafi hatsari ga ‘yan ta’adda kirar Super Tucano Jet wanda Nigeria ta saya daga Kasar Amurka

Idan ba’a manta ba, tun farkon hawan mulkin Shugaba Muhammadu Buhari Maigaskiya a 2015 ya ware makudan Biliyoyin Naira domin sayan wadannan jiragen yaki na zamani da ake takama dasu a duniya, to amma sai Gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Donald Trump a wancan lokaci taki sayarwa Nigeria makaman saboda wai sojoji suna take hakkin bil’adama

Amma da Gwamnatin Joe Biden tazo sai Gwamnatinsa ta yadda a sayarwa Nigeria jiragen, sai a shekarar 2021 Gwamnatin Nigeria ta samu nasaran sayan jiragen kuma suka iso gida Nigeria lafiya, amma ba zasu fara amfani ba har sai Amurka ta bada lasisi, to lasisin bai samu ba sai yanzu kamar yadda Dattijon kirki Maigirma Ministan Shari’a ya bayyana

Sannan kuma yana daga cikin sharadin da Gwamnatin Amurka ta gindaya wa Nigeria kafin ta sayar mata da jirgin, shine sai jami’ai daga Amurka sunzo Nigeria sun duba guraren da za’ayi amfani da jirgin wajen yakar ‘yan ta’adda da barayin daji domin kar ayi amfani da jirgin a inda bai dace ba, kuma jami’an Amurka sunzo sun duba sun tabbatar kafin Amurka ta bawa Nigeria lasisin fara amfani da jirgin

Wannan jirgin yaki Super Tucano yana gudun kusan kilomitas 600 a awa daya, sannan yana iya daukar makami ya harba da zai iya yin gudun nisan kilomita dubu 5, wato zai iya harba bomb daga Lagos ya sauka a Borno, harsashin da ake kakkabo jirgin sama baya iya huda wannan jirgin, yana iya yin awanni 8 a sararin samaniya yana barin wuta

Ministan Shari’a yace Sojojin saman Nigeria zasu kaddamar da jiragen yakin akan barayin daji da suke ta’addanci a Arewa maso yamma da sauran inda ‘yan Boko Haram suka buya domin a kakkabesu

Insha Allahu wannan shekara na 2022 zata kasance shekarar kunci da bala’i wa ‘yan ta’adda, munyi imani da Allah ba zasu wanzu suna ta’addanci ba zasu gushe watarana

Muna rokon Allah Ya kawar maba da duk wata barazana na ta’addanci a Kasarmu Nigeria Amin

Arewa Intelligence

4-1-2022

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button