LABARAI/NEWS

Nigeria yanzun nan dan ta’addan daji ya tonawa asirin sojojin

Duk wadannan Sojoji da aka kashe wa kananun sojoji ne da basu jima da shiga aiki ba idan sunje yin course a Jaji Military Contentment domin samun horo akan dabarun yaki na zamani maimakon a basu horo sai a debe su a kaisu gurin da ake yaki da bandits a yankin Arewa maso yamma

Bincike ya nuna cewa dalilin da yasa ake yin haka a Jaji Military Contentment shine masu iko basa so su cire kudi su dauki kwararru Battallion na sojoji su turasu fada da bandits saboda basu son su cire kudi wanda zasu ke biyan Battalion na sojoji kudin abinci da logistics da sauransu

shine sai su debi wadanda suka zo karban horo su turasu ana kashe su a banza don su ba za’a biyasu

Sannan yawancin wanda suke zuwa course a Jaji ba’a koya musu abinda suka je koya kowani course anayin wata 3 ne to idan an gama documentation sai a debi sojojin suje suyi wata 2 a wani guri suna dawowa sai a yaye su don ba’a son a kashe kudi ayi abinda ya kamata

Na ga sanarwan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya fitar akan harin da aka yiwa sojoji daukan mataki shine a fara bincike kan abinda na bayyana sannan masu iko da rundinar sojin Nigeria su gudanar da nasu binciken akan abinda yake faruwa a Jaji, imba haka ba to an dauko hanyar kashe aikin Soji a Nigeria

Banyi wannan bayanin don cin mutuncin wani ko bayyana gazawar wani ba, bincike ne da nake so a yi domin a tabbatar a dauki matakin da ya dace, idan akwai wanda ransa ya baci to yayi hakuriMuna fatan Allah Ya kawo mana karshen masu cin amanar tsaro da wadanda suka mayar da ta’addanci hanyar neman kudi a Nigeria

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button