Nijeriya da Saudiyya sun sa hannu kan yarjejeniyar aikin hajjin 2023

Nijeriya da Saudiyya sun sa hannu kan yarjejeniyar aikin hajjin 2023
Tawagar Nijeriya da ta isa Saudiyya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna MOU tare da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Masarautar dangane da aikin Hajjin 2023
Yarjejeniyar ta kasance ta ka’idojin da za a yi amfani da su don aikin Hajjin 2023
A wata sanarwa da shugaban yada labarai na hukumar alhazai ta kasa NAHCON ya fitar a jiya ta ce tawagar Najeriyar ta na karkashin jagorancin karamin ministan harkokin wajen kasar
Ubandawaki ya ce tawagar ta kuma hada da, Sanata Adamu Bulkachuwa, shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin kasashen waje Abubakar Nalaraba, shugaban kwamitin majalissar kan aikin hajji
shugaba/shugaban hukumar NAHCON Zikrullah Hassan da kuma wasu daga cikin mambobin hukumar da ma’aikatan NAHCON