Daga Malaman mu

NOMIIS GEE WAKILIN SHAIDAN A DORON KASA

NOMIIS GEE WAKILIN SHAIDAN A DORON KASA

Ba abin da idan na tuna shi ke kona min zuciya kamar sanda wani Shaidanin yaro mai suna Nomiis Gee da AREWA24 TV suka turo gidanmu suna min barazanar daukan mataki a kaina, laifina kawai don na ce shirin da yake yi na ZAFAFA GOMA da HIP POP yana lalata tarbiyya, a lokacin ba na Kano ina Azare Bauchi State, sai suka je gidanmu suka sami babana suka ce a ja min kunne wai idan ba haka ba za su had’a gidogar cewa da na fita kasar waje karatu, na shiga kungiyoyin ta’addanci. A farko da babanmu ya ce musu ba na nan kin yarda suka yi har sai da suka yi barazanar cewa za su tafi da shi har sai na kawo kaina kamar yadda shi baban namu ya fada min, wanda daga baya kuma sai suka tafi.

Babana a lokacin ya ba ni umarni na cire rubutun na kuma nemi afuwarsu, kuma na aikata umarnin. Sun ga Babana dattijo ne Malamin Zaure shi ne saboda samun wuri da fitsara za su yi masa wannan barazana, ba su san cewa family dinmu Babba Dan’agundi ba ne, ba su san shi din yayan su Aminu Babba Dan’agundi da su Baffa Babba da Manniru Babba ba ne har da za su yi kokarin latsa shi suna ganin kamar ba shi da gata. Allah ya ba wa wani dan iska sa’a gobe ma ya sake yin haka ya ga abin da zai faru da shi.

Kuma shi shaidanin yaron nan mai suna Nomiis Gee ba wakilin shaidan ba ne? An fada din NOMIIS GEE WAKILIN SHAIDAN A DORON KASA. A shirinsa da yake yi yana lalata mana al’umma yana shigar da matasa maza da mata harkar wake-waken kasashen turai wanda ke sabbaba wa matasa shaye-shaye, zinace-zinace da kazamar harkar nan ta neman maza wal’iyazubillah. Ga wata shaidaniyar yarinya nan mai suna Princess Mufida hotunanta na yawo na shigar banza kamar ba musulma Bahaushiya ba, nonuwanta a waje, cibiyarta da cinyoyinta duka a waje, ga maza nan masu saka sarka da d’ankunne su yi kitso a kansu tare da yin ‘Ass down’ shiga ta mashaya masu neman maza, wannan fa shi ne sakamakon abin da Nomiis gee ke aikata mana cikin al’ummarmu.

Kai da kake lalata mana al’umma ba a dauki mataki a kanka ba sai ni da nake cewa ka gyara shi ne don fitsara har ake min barazana. ‘Yayan mutane nawa ka lalata wa rayuwa ta hanyar nesanta su da karatu ko wani abu da zai amfani rayuwarsu ka dulmiyar da su harkokin wake-waken gayun kasashen turawa? Dan iskan yaro kawai mara mutunci, an fada din Nomiis gee wakilin Shaidan, wanda bai dauki mataki a kaina ba, Allah ya tsine wa uban uwarsa. Idan zafin kai kake ji da shi na fi ka, barazana ba ta taba tsayar da ni sai dai ta kara min kaimi, sanda Abduljabbar Kabara da yaransa suka yi nufin cutar da ni ba su ci nasara ba, kuma ban daina abin da nake yi kansu ba. Wallahi abun farin ciki da alfahari ne gare ni yau a ce ina rigima da mutanen banza irinsu Nomiis Gee da Abduljabbar Kabara.

Kamar yadda gwamnati ta d’auki mataki kan Abduljabbar Kabara ya zama wajibi a d’auka kan Nomiis gee wanda shi ma lalata al’umma yake yi.

Allah ya tsare mu daga sharrin mutanen banza.

Indabawa Aliyu Imam

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button