Nishadi

OBESITY (KIBA)

OBESITY (KIBA)
:::::: CM :::::

Kiba wato Obesity ajikin namiji tana nunawane a tumbinsa wato gaban cikinsa tamkar mai dauke da juna biyu. Amma mace kibarta ba aciki take nunawa ba illa a kugunta gefe da gefe wato (hips).

DON HAKA

Ka/ki nisanci duk wani maganin rage kiba da za’a ce ana sha cikin sati 1 ko 2 koma kwana 3 duk kitsen zai sauka, Sam ba hannun likitoci cikin irin wadannan magungunan koda kuwa kaga Nafdac number jiki,

Ba kwararren likitan dazai bada shawarar shan irin wadannan magungunan don haka likitoci na bada shawara ne kurum dan gane da irin yanayin ka ta hanyar tsara abinci daidai dakai da kuma karfafa ma guiwa wajan motsa jiki akalla na minti 15 zuwa 30 kullum.

YA ZAN GANE KIBATA BA MAI ILLA BACE?

Kuna iya fahimtar haka ta hanyar gwajin fadin kugunku wato (waist circumference);

  1. Namiji (men) ya zamto kasa da centimita casa’in <90cm
  2. Mace (women) ya zamto kasa da centimita tamanin <80cm

YADDA AKE

Mutum ya kwa6e ko ya daga rigarsa, ya tsaya sosai a kafafunsu ya saki jikinsa, sai asami wani yasa Tape irin na gwaji na teloli ya zagaya shi akugun yaga menene numbar da ya nuna kasa da 90cm ga maza ko sama, kasa da 80cm ga mata ko sama.
Haka ma mutum zai iya da kansa Amma de inda hali wani yaima za’a fi samun gwaji me kyau.

A dage da motsa jiki.

Drastic weight reduction is NOT encouraged because obesity can only be palliated, but NEVER cured.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button