Latest Hausa Novels

PROFESSOR YEMI OSINBANJO: BABBAN KALUBALE GA MUSULMIN NIGERIA

PROFESSOR YEMI OSINBANJO: BABBAN KALUBALE GA MUSULMIN NIGERIA

DAGA Datti Assalafiy

Mataimakin Shugaban Kasarmu Nigeria Professor Yemi Osibanjo Malamin addinin nasara ne, ya kai matsayin Bishop, babban jigo ne a cikin majalisar kungiyar mabiya addininsu na duniya ba wai a Nigeria kadai ba.

Ba shakka Professor Yemi Osibanjo yana da tsananin kishin addininsa, kuma baya wasa akan kishin addininsa, idan kuna bibiyar kafofinsa na sada zumunta zaku shaida hakan, a cikin program da yake watsawa a shafinsa na Facebook duk karshen sati sai an nunoshi a dakin bautarsu yana wa’azi, samun matsayin da yayi a Gwamnati bai hanashi watsi da kuma kyamar addininsa ba.

Kamar yadda Malam Adam Baba ya fada ne, shi dai Pastor Yemi Osinbanjo tunda ya zama mataimakin Shugaban kasa, addinin sa ne a gaban sa, kullun lalube ya ke don samun salun habbaka akidar sa ta RCCG da addininsu na nasara ba tsoro ba kunya, wannan aka rasa a tare da Musulmai.

Idan Osinbanjo ya zama Shugaban Kasar Nigeria, sai ya tabbatar da addininsu na nasara ya samu ginda zama cikin salon mulkin Nigeria, in kana ja, ka je ka yi binciken yaya ya raba kudin TraderMoney, ta yaya ya kasance akwai layin waya na (Airtel RCCG line) wanda a fakaice Kristoci kawai aka sayar wa layin?, me yasa ba Musulmai a cikin ayarin sa duk da shi Vice-President ne?

Abokan zaman mu wadanda ba Musulmai ba basa wasa da addininsu, kuma basa shakkar bayyana addininsu, idan sun samu dama a Gwamnati kokari suke su kawo ‘yan uwansu masu kaifin kishin addini su dasa su, wannan aka rasa a tare da ‘yan uwa Musulmai.

Kuma kamar yadda Professor Farooq yayi bayani a cikin dalilansa na hudu yace: Osinbajo mutun ne mai fara’a amma mai guba, mai kiyayyar Islama wanda yake tufatar da son zuciya da baka, Yana cudanya da musulmi ne kawai saboda manufarsa ta siyasa. Shiyasa fa a kaf cikin masu tsaron lafiyarsa babu Musulmi ko guda daya, duk wani sensitive guri dake ofishinsa babu Musulmi.

Abokan zaman mu wadanda ba Musulmai ba basu taba yadda su fifita siyasa akan addininsu ba, fifita siyasa akan addini sai Musulmai, Sheikh Albaniy Zaria yace idan Musulmi yace maka a siyasa ba ruwansa da addini to da gaske yake saboda wauta, amma idan wanda ba Musulmi bane ya fada maka haka to karya yake, domin a lokacin da yake fadin haka idan ka duba wuyansa zaka ga ya rataya sarkan cross, a cikin office dinsa akwai Littafin Injila.

Ta kowace fuska Osibanjo baiyi laifi ba, damace ya samu kuma ya kafa addininsa, ba shakka idan ya zama Shugaban kasa duk wata hukuma na tsaro sai an rinjayar da wadanda ba Musulmai ba, hakanan duk wata ma’aikata, a gurin diban jami’an tsaro da samar da guraban aiki za’a yiwa Musulmai muguwar illa, ajandace irin wanda akayi a Kasar Kamaru.

Jama’a ku bincika, tun daga lokacin da shugaban Kasar Kamaru na farko Marigayi Alhaji Ahmad Ahidjo yayi sakainar kashi ya mikawa Paul Biya wanda ba Musulmi ba shugabanci aka illata Musulmai a Kamaru, ta yadda zaiyi wuya Musulmi ya sake zama shugaban kasa a Kasar Kamaru.

Kar mu ga laifin Osibanjo damace suka samu, kuma sunyi amfani da damar a yadda ta dace, ina ji mana tsoro idan suka kafa Gwamnati zaiyi wahala Musulmi ya sake zama shugaban kasa a Nigeria, domin duk hanyar da ya kamata su bi sai sun bi sun toshe, kowa ya tsaya yayi tunani akan wannan, kuma a tuntubi tarihin abinda ya faru a Kasar Kamaru.

Akwai ‘yan uwa da na san suna goyon bayan Osibanjo saboda an biyasu kudi ne an basu kwangila, akwai wadanda suna goyon bayansa saboda watakila za’a bawa wanda suke so matsayin mataimakin shugaban kasa, amma ka sani ya kai dan uwa Musulmi, duk lalacewar dan uwanka Musulmi yafi wanda ba Musulmi ba, idan ka fifita wanda ba Musulmi ba akan Musulmi baka da hujjar da zaka kare kanka a gaban Allah, ko da wasa ka kiyayi goyon bayan abinda zai mayar da Musulunci baya.

Muna rokon Allah Ya daukaka Musulunci da Musulmai a Nigeria da duk duniya Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button