Qalu innalillahi wa’inna’ilahiraji’un ; duniya ina zaki da mu

Tun bayan ayyana daina fito da sababbin kudi a kasa Nigeria yan ta’adda suka shiga fargaba wajen samun sababbin kudi
Wasu yan ta’adda sun shiga hannu bayan da suke kokarin fitowa da wasu makudan kudi don chanzin su zuwa sabbin kudi
Hukumar yan sanda ce dai ta sanar da wannan kamu da sukayi inda suka kwace kudi kimanin Naira miliyan dari tare da wasu gugayen makamai
Matsalar rashin tsaro dai na cigaba da daukar wata sabon salo lamarin da ya ke cigaba da haifar da durkushewar tattalin arziki a yankunan da abun ya shafa
Haka kuma manyan hanyoyin kasar nan suka zama barazana ga Al umma biyo bayan yadda ake dauke mutane kamar wasu dabbobi
Wannan matsala ya rashin tsaro dai ta dade tana ciwa Talakan wannan kasa tuwo , daga wani bangaren kuma tsadar kayan masarufi na neman jefa Talakan kasar nan cikin yunwa
Duk da irin wannan wahala da talaka ke sha a wanna kasa hakan bai hana shugabanni kawo karshen matsalar tsaro ba wanda ta kasance babban abinda ke samun sa