Daga Malaman mu

RADADIN RABUWA DA MOSIYIYA

Irin Radadin Kunar Zuciya Da Maza Suke Fadawa Bayan Macen Da Suke So Ta Rabu Dasu:

 

Mata suna dauka sune suke fiskantar kunar zuciya a lokacinda namiji yace baya sonsu. Abun ba haka yake ba. Maza suma suna shiga wahala matuka bayan mace tace musu ta daina soyayar dasu.

 

Ga wasu radadin da zafin kunar zuciya da masa ke shiga idan mace ta rabu dasu.

 

1:Kidemewa: Ko yana sane ko ya zo musu a bazato. Duk namijin da macen da yake soyaya ko aure tace su rabu dole sai ya kedime a wannan lokacin.

Maza suna shiga matukar damuwa su rasa abunda suke yi ko suke ciki na dan wani kwanaki.

 

2: Zaiyi Duk Iya Kokarinsa Domin Samun Kanki: Namijin da ya rasa soyayar macen da yake so, zai yi duk wani kokarin na ganin cewa ya shawo kanki. Ba zai taba hakura farat daya ba har sai yayi iya kokarinsa ya kasa.

 

3: A Lokacin Zai Ji Sabuwar Soyayyar Ki: A lokacinda mace tacewa namiji kowa ya kama gabansa, a wannan lokacin mace take kara shiga ransa fiye da a baya. Wannan yasa rabuwa dake zai cutar masa da zuciya yaji shifa yanzu ya fara sonki.

 

4: Zai shiga Kadaici: Duk irin walakancin da namiji yake miki a lokacinda kuke soyayya, kina cewa baki sonshi zai ji kadaicinki ya kamashi koda kuwa kullum sai ya koreki kamin ku rabu. A lokacin ne zai ji idan zaku wuni ku kwana tare bazai gaji dake ba.

 

5: Zaki Rika Masa Gizo gizo: Kina rabuwa da saurayinki da yake sonki zaki soma yi masa gizo gizo. Duk macen daya gani sai yaga kamar kece. Idan kuma yaga mai yanayinki sai ya ji sanyi a ransa. Idan zai samu dama sai ma yayi mata magana.

 

6: Zai Daina Sha’awar Soyayya: A lokacinda mace ta rabu da maisonta, zai ji soyayya ya fice masa a rai. Zai ji duk wacce zai fada soyayya da ita za a sake kumawa.

 

7: Zai Tsargu: Da zaran budurwa ta rabu da wani mai sonta ta koma soyayya da wani. Zai tsargu da tunanin mai wancan ya fishi da shi har zata rabuda shi ta kama soyaya da wani.

 

Maza sukan kasa fahimtar kansu bayan wani ya kasasu. Wasu idan wanda ya kwace masa budurwan abun hawa gareshi, zai soma tunanin mallakar irin wannan abun hawa. Haka idan kwalliya ko kyauta aka fishi zai so ya gyara da zai sake samu wata damar daga wajenta.

 

8: Neman Na Kusa Dake: Kina rabuwa da saurayinki zai shiga neman na kusa dake domin su sasanta ku.

A lokacin ne duk wani na kusa dake dayasani harma da wadanda bai sani ya rika musu sintiri domin su shiga lamarin.

 

9: Saurin Fushi: Mazan da aka kwace musu budurwa suna fadawa cikin saurin fushi na wasu kwanaki.

Abu kadan za a musu su soma fada da zage-zage. Irin wadannan mazan a sama suke na saurin fushi.

 

10: Zai Rasa Abunda ake Masa Dadi: Namijin da mace tace masa bye bye a bazata, zai rasa abunda ke masa dadi a rayuwarsa.

 

Sai dai bambamcin kunar zuciya tsakanin Maza da Mata a rabuwar soyayya, su mazan sunada jimriyar da ba kowa bane zai fahimci suna cikin kunar zuciya ba. Hakan yasa ake ganin kamar mata kadai ke shan wahalar heartbreaking ba.

 

Kowace mace tanada dalilin rabuwarta da nanijin da suke soyayya da shi.

 

Idan zaki rabu da mai sonki, kada ki rabu da masoyinki ba tare da wani kwankwaran hujja ba.

 

Bawa juna uzuri a matsayinku na masoya masu fatan aure, kada ya zamemuka

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button