Rahama Sadau a karo na biyu zata sake fitowa a Film din India

Rahama sadau ta sake fitowa a cikin wani sabon Film din India tun bayan da ta fito a cikin Film din India ta na farko kuma aka fassara shi da suka garkuwa a harshen Hausa
Rahama sadau wacce ta kasance tsohuwa jaruma a masana’antar kannywood ta sake fitowa a cikin wani sabon Film wanda ya kasance Film din ta na biyu a kasa India
Fitowar ta rahama sadau ta biyo bayan da ake cigaba da cece kuce kan Film din ta na farko inda ake ta magana kan cewa sau daya aka hango jarumar a cikin Film din
Sai dai kuma a cikin wannan sabon Film din wanda tsohuwar jaruma kannywood din ta ke ciki ta kasance daya daga cikin jaruman Film din ba kamar wanda yayi a baya ba
Sai dai kuma nuno rahama sadau rungume a jikin wani jarumi India na cigaba da daukar hankali mutane inda suke cigabd a tofa albarkacin bakin su kan wanna batu
Duba da cewa ita musulma ce hakan ya sanya wasu mutane cigaba fada ma ta gaskiyar cewa bai dace abun da take ba ,sai dai kuma jarumar ba jin wanna magana tasy’u take ba