Rahama Sadau Ta Ƙara Shillawa India Domin Gabatar Da Wani Shirin Film

Rahama Sadau Ta Ƙara Shillawa India Domin Gabatar Da Wani Shirin Film
Fitacciyar Jarumar fina-finan Najeriya da Indiya Rahama Sadau ta ƙara shillawa indiya domin kara daukar wani Film ɗin
tun kwana biyu da suka gabata ne dai ta isa ƙasar ta indiya kamar yadda ta bayyana a shafin ta na facebook da kuma na tweeter da IG
Tun bayan korar ta daga finafinan Kannywood ko shekarun baya ma Jarumar taje Amerika sannan taje Indiya inda ta gudanar da wani Film tare da jaruman can lamarin da ya bawa al’umma mamaki inda akai tunanin can zata koma kafin daga bisani ta dawo Najeriya
A wannan karon ma taje India kuma tuni har sun fara daukar wani Film wanda ba’a bayyana sunan sa inda ta fitar da hoton su tare jarumi a masana’antar Bollywood Rajni Eshduggall