LABARAI/NEWS

Dalilin da yasa nace niba Cikakkiyar budurwa bace, Rahama Sadau

Dalilin da yasa nace niba Cikakkiyar budurwa bace, Rahama Sadau

Rahama Sadau ta bada labarin yadda ta rasa budurcin ta tun Tana Yarinya.

– Tayi wannan bayanin ne yayin da take yin fira da majiyar mu a satin da ya gabata.

– Ta ce an taba yi mata fyade ne sadda tana yarinya karama ne.

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood Rahma Sadau ta yi karin haske game da yadda ta rasa budurcin ta kamar dai yadda ta taba bada labarin cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace ba a watannin baya.Jarumar dai ta yi wannan karin haske ne yayin da take yin fira da majiyar mu ta Mujallar fim a satin da ya gabata karon farko tun bayan dawowar ta daga kasar Turkiyya inda taje karatu.

Jarumar ta bayyana cewa maganar da tayi a watannin bayan na cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace ba wai tana nufin ta taba zina ba ne domin ita hasali ma ba ta taba zina ba tun da Allah ya halicce ta.

Jarumar ta kara da cewa abunda take so ta fadawa duniya shine an taba yi mata fyade ne sadda tana yarinya karama kuma a lokacin ne ma ta rasa budurcin na ta kamar dai yadda ta fada.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa muhawara ta zafafa a watannin baya lokacin da jarumar ta bayar da ansa ga wani masoyin ta da ya tambayeta matsayin budurcin ta a kafar sadarwar zamani ta Instagram inda ta ba shi ansa da cewar ita ba cikakkiyar budurwa bace.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button