LABARAI/NEWS

RAHOTON AMURKA A MIZANI NA ADALCI

RAHOTON AMURKA A MIZANI NA ADALCI

Bayan da ofishin jakadancin Amurka da Burtaniya dake Abuja Nigeria suka fitar da sanarwa akan munanan harin ta’addanci da zasu iya faruwa a sassan Nigeria musamman birnin tarayya Abuja, masu iko da tsaron Nigeria sun hakikance akan cewa babu komai, ba wata barazana

Na saurari wani jawabi da Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya yayi, inda yake bawa ‘yan Nigeria tabbacin cewa zai kawar da matsalar tsaro a sauran watanni 6 na mulkinsa da ya rage

To sai mu duba mu gani ta ina zai fara:
1-Gyara jami’an tsaron?
2-Wadata jami’na tsaron da kayan aiki na zamani?
3-Kakkabe manyan maciya amanar tsaro a cikin shugabannin tsaro?
4- Dakile hanyoyin da ‘yan ta’adda suke samun makami, man fetur, communication, miyagun kwayoyi da ababen hawa?

A cikin wadannan matsaloli guda guda hudu babu guda daya da za’a iya magancewa a watanni 6, don haka maganar Shugaba Buhari kamar bai san abinda yake faruwa bane

Mu dubi rahoton Amurka da Burtaniya a mizani na adalci, sannan mu dauki harin jirgin kasan da ya kwaso fasinja daga Abuja zuwa Kaduna a matsayin case study, da abubuwan da suka faru bayan harin, hari ne wanda tunda aka kafa kungiyoyin ta’addanci a Nigeria basu taba harin da suka samu kudi mai yawa kamarsa ba, sun karbi Biliyoyin Naira na kudin fansa

Sannan a tarihin Nigeria, ba’a taba samun lokacin da ‘yan ta’adda suka shiga babban birnin tarayya Abuja sukayi hari a gidan yari mafi tsaro kamar a wannan lokaci ba, wannan hujjace da take tabbatar da sunyi karfi, tare da fahimtar cewa ‘yan ta’addan suna da wakilansu a cikin manyan jami’an tsaro wadanda suke taimaka musu da bayanan sirri

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button