LABARAI/NEWS

RANA A DAKIN ALLAH: Masana a Saudiyya sunyi hasashen cewa a gobe Asabar Rana zata tsaya cak a daidai tsakiyar dakin Ka’abah da misalin karfe 12:18 na rana agogon Makkah.

RANA A DAKIN ALLAH: Masana a Saudiyya sunyi hasashen cewa a gobe Asabar Rana zata tsaya cak a daidai tsakiyar dakin Ka’abah da misalin karfe 12:18 na rana agogon Makkah.

Duk inda saitin rana yake a daidai wannan lokacin to nan ne Alkibla, Ranar zata tsaya daidai Alkibla. A Najeriya wajajen karfe 10:27 na safe za a duba.

📸: Haramain Sharifain

KARIN BAYANI: Shin Masallacin da Kake Sallah yana fuskantar Alkibla? Ko kuma a Dakin da Kake Sallah da sauran wuraren da ake Sallah suna fuskantar Alkibla?

To ga dama ta samu a gare ka yadda zaka tabbatar da inda kake Sallah yana fiskantar Alkibla ko kuma baya fiskanta.

Abinda ake nufi da Alkibla shine dakin Ka’aba na Makkah.

Daga Adamu Ya’u Dan America

Idan Allah ya kaimu gobe Asabar (28/05/2022) da misalin karfe 10:18 na safe agogon Nigeria, Rana zai daidaita da saitin saman dakin Ka’aba.

Saboda haka a daidai wannan lokacin idan ka tsaya a gaban Masallacin anguwan ku ka fiskanci Rana kaga Masallacin yana Fiskantar Rana to Masallacin yana fiskantar Alkibla, idan kuma kaga masallacin bai fiskanci Rana ba to Masallacin baya fiskantar Alkibla, Haka a cikin Dakin da kake yin Sallah da sauran wuraren da ake Sallah.

Idan Allah ya sa a gobe Asabar ka manta lokacin ya wuce baka samu ka duba ba ko kuma Hadari ya rufe sama a inda kake, to akwai wani dama na sake dubawa a ranar Asabar (16/07/2022) misalin karfe 10:27am na safe wato bayan Sati 7 kenan.

A gaskiya mafi yawan Masallatan mu basu fiskantar Alkibla, yawanci suna fiskantar kasar Ethiopia da Arabian Sea ne.

Saboda yawancin mutane anan Nigeria idan zasu yi Sallah Gabar Direct kawai Suke fiskanta, Alhali ba Direct bane yakamata su fiskanta ba, ya kamata su dan Karkace ta Hagu kadan, saboda mu a Nigeria Makkah yana Arewa maso Gabas ne, ba Gabas Direct ba.

Da fatan Allah ya sa mu dace Ameen Summa AAl-Ameen Abubakar GainiAl-Ameen Abubakar GainiAl-Ameen Abubakar GainiAAl-Ameen Abubakar GainiGAl-Ameen Abubakar Gaini

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button