ylliX - Online Advertising Network RARARA DA GANDUJE AYIWA DAUDA RARA ADALCI - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

RARARA DA GANDUJE AYIWA DAUDA RARA ADALCI

RARARA DA GANDUJE AYIWA DAUDA RARA ADALCI.

Cikin kwankinan inata ganin maganganun jama’a akan wani jirwaye da rara yayi a cikin wata waƙa mai taken (APC CE A SAMAN PDP) inda jama’a ke ganin baiken rara domin yayiwa Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar ganduje shaguɓe a wakar.

Idan za’ayi wa rara adalci Akwai bukatar mutum yasan meye Dalilin da yasa rara ya barranta kanshi da APC a matakin jihar kano! Lokacin primary Election rara da mutanensa sunso a basu Kujeru biyu cikin samada sittin, amma APC taƙi amincewa da buƙatarsu, kaga an nuna musu basuda amfani dasu da jama’arsa baki ɗaya, wannan yasa suka tafi jami’yarsu Shaaban sharada kuma aka bawa Mutanen biyu takara, mutanen sune ; Adam Abdullahi Adam (Abale) Aminu Ladan Abubakar (Alan waƙa).

Wannan yasa suka tare Duk wata basirar su domin bawa Shaaban sharada Gudunmuwa, kuma Gudunmuwar ta Isa ko’ina. Hakan yasa ganduje ya hasala, ya fara faɗin yan maganganu akan tawagar rara, batare da ya tuna irin halarci da rara yayi musu ba, lokacin babu mai iya Magana duk APC ta kano sai Rara da mutanensa.

Tun farko ganduje ya haddasa komai, domin yasan Irin tasirinsu, amma ya nuna musu basuda amfani bakiɗaya, yake musu kallon kamar su bakomai bane, ko Babu su Komai normal ne, sai suka gwada mishi sunada nasu tasirin.

Wallahi duk Wanda yasan darajar kanshi, kuma yasan Siyasa, iyakar wannan matakin dasu Dauda Rara suka ɗauka zai ɗauka, domin ribar siyasa a duniya ake biyanta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button