ylliX - Online Advertising Network Rashin Halartar Taron Arewa Joint Forum da Kwankwaso Yayi Shine Abu Mai Kyau. - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Rashin Halartar Taron Arewa Joint Forum da Kwankwaso Yayi Shine Abu Mai Kyau.

Rashin Halartar Taron Arewa Joint Forum da Kwankwaso Yayi Shine Abu Mai Kyau.

A taƙaice, an ƙirƙiri gamayyar ƙungiyoyin Arewa (Arewa Joint Forum) ne domin haɗa-kan al’ummar Arewa da kuma ƙoƙarin kawo cigaba Arewa ta fuskar ilimin zamani, tsaro, lafiya, noma, da duk wani abu da zai ɗaukaka darajar yankinmu na Arewa. Waɗanda suka bayarda gudunmawa tare da assasa wannan ƙungiya sune, Sir Ahmadu Bello Sardauna, Sir Abubakar Tafawa Balewa, Malam Aminu Kano, Alhaji Kashin Ibrahim da sauransu.

Kamar yadda na bayyana da farko babban muƙasudin samuwar wannan ƙungiya shine nemawa Arewa mafuta. Sai ga shi kuma muna tsari na siyasa (democracy). Wanda ta hanyar zaɓe ne kawai mutane za su fitar da shugaban da zai jagorance su a matakin ƙasa da sauran matakai daban-daban.

Abin takaici, wannan ƙungiya ta “Arewa Joint Forum” ta fara sauya salo maimakon ta ɗora bisa kan layin da magaban baya suka kafa ta. Misali, Atiku da Kwankwaso suna neman takar shugabancin Nigeria, yayinda babban alhakin wannnan ƙungiya shine ta haɗa-kan Arewa ta hanyar zaɓo zaƙaƙuri a loƙacin zaɓe wanda zai kawo cigaba a Arewa dama Nigeria baki dɗaya.

A wannan karon sun nuna rashin adalci da rashin kishin Arewa. Domin, mun samu bayanai ta ɓangarori daban-daban cewa Atiku za su goyawa baya. Ni kuma a lissafi na, duk mutumin da yake kishin Arewa, cigaban Arewa da al’ummar Arewa bisa irin halin da suka shiga, ba zai bar Kwankwaso ya ɗauki Atiku ba. Saboda Kwankwaso shine na talakawa, a koda yaushe yana kusa da talakawa, kuma yana da “vast experience” akan halin da talakawa musamman na Arewa suka shiga.

Wannan shine dalilin da ya sanya Kwankwaso ya bayyana cewa ba zai halarci taron ba, kamar yadda mai magana da yawunsa Hon. Abdulmumin Jibril ya bayyana. Akwai dalilai masu yawa, amma ya kamata mutane su fahimci cewa rashin zuwan Kwankwaso, yana da nasaba da yunƙurin da wannan ƙungiya take wajen raina wayon ƴan-Arewa ta hanyar goyon bayan Atiku, wanda bai damu da damuwar talakawan Arewa ba.

Kwankwaso shine cikakken masoyin Arewa da yan Arewa. Domin ƙafa da ƙafa jaye Ogun loƙacin rikicin Ile-ife, ya nuna soyayya ga ƴan Arewa ta hanyar nemo musu ƴan-ci tare da basu tallafi. Yaje manyan kasuwanni biyu a Jihar Legas, Mile-12 da Alabarago, ya karɓo ma ƴan Arewa masu neman abinci a wuraren yan-ci. Me Atiku ya taɓa yi makamancin wannan?

Don haka Kwankwaso shine masoyinmu, kuma na tabbata yana kishinmu. Al’ummar Arewa sun haska, sun kuma fahimci alkhairin da yake tattare da Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, don haka babu wata ƙungiya da zata raina musu hankali akan cewa su zaɓi Atiku. Ƴan Arewa sun waye. Kuma rashin zuwan Kwankwaso taron ba zai hana al’ummar Arewa bashi miliyoyin ƙuri’u a ranar zaɓe ba. Insha Allah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button