ylliX - Online Advertising Network Rikici a kungiyar CAN biyo bayan sanya manyan Bishop yakin neman Zaben Tinubu-kashim - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Rikici a kungiyar CAN biyo bayan sanya manyan Bishop yakin neman Zaben Tinubu-kashim

Rikici a kungiyar CAN biyo bayan sanya manyan Bishop yakin neman Zaben Tinubu-kashim

A makon da ya gabata ne aka fara samun tarzoma a cikin kungiyar Kiristocin Najeriya CAN.

Hakan na da nasaba ne da matsayin CAN na nuna bangaranci da kuma tikitin tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar (APC) wanda acewar su yadda aka raba mukamin akwai son zuciya daga wasu manyan malaman addinin kirista.

Sai dai shugabancin kungiyar Kiristocin ya tashi tsaye wajen ganin an gyara tsatsauran ra’ayi tare da ruguza lamarin da ke barazanar wargaza kungiyar da mabiya addinin kirista.

kwamitin yakin neman zabe na Tinubu/Shettima 2023, wanda ke dauke da sunayen akalla manyan hafsoshi takwas da mambobin kungiyar CAN.

Daga cikin su akwai mataimakin babban sakataren kungiyar CAN, Apostle Biodun Sanyaolu, wanda aka dauka a matsayin mataimakin kodineta, hulda da masu ruwa da tsaki; Shugaban kungiyar CAN na jihar Legas, Bishop Stephen Adegbite (mamba); Daraktan Shari’a da Hulda da Jama’a na CAN na kasa, Barr. Comfort Chigbue (memba); da Mista Testimony Onifade, tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban CAN, Rev Samson Ayokunle (memba).

Sauran sun hada da Dr Victor Ivoke, Mataimaki na Musamman ga Archbishop Daniel Okoh, Shugaban CAN na yanzu (mamba); Tsohon Daraktan Shari’a da Hulda da Jama’a na CAN, Kwamkur Samuel (mamba) da Farfesa Para-Mallam (mamba).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button