ylliX - Online Advertising Network Rikicin Boko Haram ya yi sanadin rayuka 100,000, tare da hasara ta tiriliyan N3.24 - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Rikicin Boko Haram ya yi sanadin rayuka 100,000, tare da hasara ta tiriliyan N3.24

Rikicin Boko Haram ya yi sanadin rayuka 100,000, tare da hasara ta tiriliyan N3.24

Babban hafsan tsaro na Najeriya Janar Lucky Irabor,ya ce rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar mutum 100,000, yayin da ya raba mutum miliyan biyu da muhallansu tare kuma da janyo hasarar kusan naira tiriliyan 3.24.

a Najeriya ta ruwaito mista Iroba na fadin haka a ranar Talata a lokacin rufe bikin bitar ayyukan ministocin kasar da aka gudanar a Abuja babban birnin kasar.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumomin sojin kasar sun karbi naria tiriliyan 2.5 a kasasfin kudi na shekaru bakwai da suka gabata, amma duk da haka sun yi kokarin inganta ayyukan harkokin tsaron cikin gida.

Sai dai kuma ya nuna nadama kan kudin da aka ware wa hukumomin sojin kasar, wanda ya ce kashi 35 ne cikin 100 na abin da hukumomin ke bukata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button