LABARAI/NEWS

Rikicin Fulani da kambari ya jawo Sanadiyyar rasa rayuka a jihar Neja

Rikicin Fulani da kambari ya jawo Sanadiyyar rasa rayuka a jihar Neja.

Wani Rikicin Fulani da Kambari Yayi Sanadiyyar Rasa Rayukan Mutane 2, Tare da kona Ofishin ‘Yan Sanda a Jihar Neja.
Aƙalla mutane biyu aka kashe sakamakon rikicin fili da ya ɓarke tsakanin Kambari da Fulani a garin Salka da ke ƙaramar hukumar Magama ta jihar Neja

Lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata saboda mallakar fili ne ya yi sanadiyyar ƙona ofishin ‘yan sanda, da kuma wasu matsygunin Fulani kusan talatin.

tattaro cewa a baya Fulanin sun sayi fili a yankin tun shekaru da suka gabata wanda bai yi wa mutanen ƙauyen da suka kai ga rikicin daɗi ba.

Majiya mai tushe ta shaidawa wakiliyar mu cewa an fara cece-ku-ce a lokacin da ɓangarorin biyu suka ziyarci filin domin sasantawa, a lokacin ne wani Bafulatani ya raunata ɗaya daga cikin abokin hamayyarsa da yankan rago, shi ya sa aka fara rikicin.

Sakataren gwamnatin jihar, SSG, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan yadda lamarin ya faru, inda ya ce an baza jami’an tsaro a yankin domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Har ila yau, kwamishinan tsaro na cikin gida da ayyukan jin kai, Emmanuel Umar, ya kara tabbatar da faruwar lamarin lokacin da aka tuntuɓi gwamnatin jihar inda ya ce gwamnatin jihar na kan gaba wajen ganin an samu kwanciyar hankali a yankin.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button